الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Masu neman a zauna lafiya sun yi gagarumar zanga-zanga a Amurka kan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza

Kungiyar Yahudawa ta Jewish Voice for Peace ta gudanar da zanga-zanga a manyan biranen Amurka a dare na 8 na cikin al'adun Yahudawa na Hanukkah inda suke nema Isra'ila ta daina yakin da take yi a yankin Gaza na Falasdinawa Wata kungiyar Yahudawa da ke neman Isra'ila ta daina kai hare-hare a Gaza...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:17 ص
Masu neman a zauna lafiya sun yi gagarumar zanga-zanga a Amurka kan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza
لمحة سريعة

Kungiyar Yahudawa ta Jewish Voice for Peace ta gudanar da zanga-zanga a manyan biranen Amurka a dare na 8 na cikin al'adun Yahudawa na Hanukkah inda suke nema Isra'ila ta daina yakin da take yi a yankin Gaza na Falasdinawa Wata kungiyar Yahudawa da ke neman Isra'ila ta daina kai hare-hare a Gaza...

Kungiyar Yahudawa ta Jewish Voice for Peace ta gudanar da zanga-zanga a manyan biranen Amurka a dare na 8 na cikin al'adun Yahudawa na Hanukkah inda suke nema Isra'ila ta daina yakin da take yi a yankin Gaza na Falasdinawa Wata kungiyar Yahudawa da ke neman Isra'ila ta daina kai hare-hare a Gaza ta gudanar da jerin zanga-zanga a birane takwas na Amurka ranar Alhamis a kwana na takwas na bikin al'adun Yahudawa mai suna Hanukkah, inda suka toshe hanyoyi da gadoji a biranen Washington da Philadelphia. A Washington, kungiyar Yahudawa ta Jewish Voice for Peace ta ce masu zanga-zanga kimanin 90 sun toshe wata babbar hanya a yankin New York Avenue da ke arewa maso yammacin babban birnin kasar. 'Yan sanda sun ce masu zanga-zangar sun toshe wasu manyan tituna na New York Avenue da North Capitol Street sannan suka bukaci mutane su yi amfani da wasu hanyoyin. "A dare na 8 na bikin Hanukkah, a birane 8 da kuma gadoji 8," in ji kungiyar Jewish Voice for Peace a sakon da ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya ake kira Twitter. "Mun taru a nan, da kuma a fadin kasar nan, inda muke da yawa, kuma muna cewa ba mu yarda a ci gaba da kai hare-hare ba." An yi manyan gangami a Boston, Atlanta, Chicago, Minneapolis, Seattle da Portland da Oregon. 'A bar mutanen Gaza su sarara' A Philadelphia, masu zanga-zanga kusan 200 sun toshe manyan hanyoyi masu lamba I-76, amma an kama mutum fiye da 30, kamar yadda ganau suka gaya wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da aka rubuta cewa: "A bar mutanen Gaza s usarara" da kuma "Ba da yawunmu ake yaki ba."