Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Masu hakar ma’adanai kusan 300 sun makale a karkashin kasa a Afirka ta Kudu

Kakakin kamfanin haƙar ma’adanan na Sibanye ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci. Kamfanin haƙar ma’adanai na Sibanye Stillwater ya ca ana ƙoƙarin ceto mutane 289 da suka maƙale a wajen haƙar ma’adanan zinare na ka...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:17
Masu hakar ma’adanai kusan 300 sun makale a karkashin kasa a Afirka ta Kudu
Kwa muhtasari

Kakakin kamfanin haƙar ma’adanan na Sibanye ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci. Kamfanin haƙar ma’adanai na Sibanye Stillwater ya ca ana ƙoƙarin ceto mutane 289 da suka maƙale a wajen haƙar ma’adanan zinare na ka...

Kakakin kamfanin haƙar ma’adanan na Sibanye ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci. Kamfanin haƙar ma’adanai na Sibanye Stillwater ya ca ana ƙoƙarin ceto mutane 289 da suka maƙale a wajen haƙar ma’adanan zinare na kamfanin da ke Kloof kusa da birnin Johnnesburg. “Muna tabbatar da cewa an samu haɗari a Kloof 7, kuma mun duƙufa wajen ƙoƙarin samar musu da hanyar fitowa, inda daga nan kuma za mu fito da ma’aikatan,” kamar yadda kakakin kamfanin na Sibanye ya bayyana a ranar Juma’a. Kakakin ya ce duka ma’aikatan suna cikin ƙoshin lafiya, kuma mun san inda suke, sannan kamfnain yana ƙoƙarin tura musu da abinci. “Muna fatan cewa za a warware matsalar zuwa tsakiyar ranar yau,” a cewar kakakin. Tun da farko, Ƙungiyar Masu Haƙar Ma’adanai ta ƙasar (NUM) ta ce ta samu rahotannin hatsarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe goma na dare a ranar Alhamis.