Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Masar na ƙoƙarin taimakon Falasɗinawa ne, ba wai katange su akan iyaka ba

Wani mai nazari ya ce soki burutsu da karin gishiri a miya ne kawai ake yi game da cewar wai Masar na shirin kafa wani yankin mafaka a Falasdinawan da suka gudu daga Rafah. A yayin da Isra'ila ke ci gaba da yin barazanar kai hare-hare a Rafah, Masar kuma na fuskantar suka kan rahotannin da kafafe...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:17
Masar na ƙoƙarin taimakon Falasɗinawa ne, ba wai katange su akan iyaka ba
Kwa muhtasari

Wani mai nazari ya ce soki burutsu da karin gishiri a miya ne kawai ake yi game da cewar wai Masar na shirin kafa wani yankin mafaka a Falasdinawan da suka gudu daga Rafah. A yayin da Isra'ila ke ci gaba da yin barazanar kai hare-hare a Rafah, Masar kuma na fuskantar suka kan rahotannin da kafafe...

Wani mai nazari ya ce soki burutsu da karin gishiri a miya ne kawai ake yi game da cewar wai Masar na shirin kafa wani yankin mafaka a Falasdinawan da suka gudu daga Rafah. A yayin da Isra'ila ke ci gaba da yin barazanar kai hare-hare a Rafah, Masar kuma na fuskantar suka kan rahotannin da kafafen watsa labarai suka fitar na cewa tana shirin gina katanga akan iyakarta da manufar katange Falasdinawan da hare-haren soji suka raba da matsugunansu. An dinga yawan azarbabi game da sukar da ake ma Masar, a yayin da kasar ke ci gaba da nuna adawa da tirsasawa Falasdinawa su bar matsugunansu, kuma ta ke kokarin ganin Isra'ila ta dakatar da mamaya. Kasar na kuma shirin tunkarar kusantar iyakarta, tane aikin taimaka wa Falasdinawa mabuƙata. Da yake mayar da martani kan shirin kan iyakar a makon da ya gabata, Diaa Rashwan, shugaban Hukumar Sadarwa ta Masar (SIS) ya ce, raba Falasdinawa da matsugunansu "na nufin hana tabbatar da burinsu, kuma barazana ce kai tsaye ga ƙarfin iko da tsaron kasar Masar." Wasu hotuna da bidiyo da kungiyoyin sanya idanu da mafufuta suka fitar sun nuna ana gudanar da manyan ayyukan gini a bangaren Masar na kan iyakar Rafah, ciki har da katangun kankare da kuma baje kasa. Amma babban jami'in diplomasiyyar Masar ya yi watsi da zargin, yana mai cewa 'Masar na gina wani waje ne kawai na karbar Falasdinawan da aka raba da matsugunansu". "Ba za mu kalli wannan shaci fadi ba. Kuma za mu ci gaba da yin kira ga dukkan kawayenmu, dukkan wadanda suka fahimci rikita-rikita da hatsarin da ke tattare da wannan batu, sannan muna bayyana cewa dole za a samu sakamako mara daɗi idan aka raba mutane da matsugunansu," in ji Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry. Hoton da tauraron dan adam ya dauka da ke nuna ana gina katanga a kan iyakar Masar-Gaza da ke kusa da Rafah, February 15, 2024 (Maxar Technologies/Handout via REUTERS). Gaskiya dai a bayyane take. Alkahira na bayar da fifiko wajen gina "yankin ajiye kayayyaki" da aka shirya samarwa a Rafah da manufar samun damar gudanar da ayyukan jinƙai. Yanayin jinƙai da bukatar kula da lafiya sun girmama sosai fiye da kowane lokaci, inda shugaban WHO ya kira Gaza da "yankin mutuwa." Shirin da Isra'ila ke yi na kai hari Rafah - yankin da ke dauke da Falasdinawa 1.4 da aka raba da matsugunansu - ya janyo yawaitar tantancewa a ayyukan tsare kan iyaka da Alkahira ke yi, wanda tun tsawon watanni ake ganin kwararar jama'a zuwa yankin. Kwanaki bayan Isra'la ta kaddamar da hare-hare a Gaza a watan Oktoba, Alkahira ta bayyana karara yadda take adawa da duk wani yunkuri na samar da "yankunan zaman lafiya" ga Falasdinawan da aka tirsasawa barin matsugunansu. Wannan matsaya ba ta sauya ba, a yayin da Masar ta gargadi Ƙasashen Yamma da na Larabawa kan 'hatsarin da ke tafe' idan aka tirsasawa Falasdinawa barin yankunansu, kuma ta bayyana hare-haren Isra'ila a Rafah da cewa ibtila'i ne da zai yi muni sosai. Adawar da Masar ta nuna ga hare-hare ta kasa na Isra'ila na da muhimmanci sosai ga 'yancin Falasdinawa. Duba ga tarihin Isra'ila na mamaye yankuna da korar jama'a, ba za su taɓa bai wa Falasdinawa damar koma wa yankunansu ba. Wani abu da ya gabata da ke da muni shi ne balahirar da ta afku a Nakba a 1948, inda aka tirsasawa Falasdinawa 700,000 suka bar matsugunansu. Ba a taba bayar da wani tabbaci a yankin na ganin sun koma gidajensu ba. Yanayin kwarar jama'a da gudun hijira da ake yi a yanzu ba yanayi ne da Masar da wasu kasashe za su amince da shi ba, ciki har da Turkiyya, wadda ta ke adawa da korar jama'ar Gaza daga yankunansu, kuma take aiki tare da Alkahira don hana kai hare-hare Rafah. Duk wani nau'i na raba jama'a da muhallansu, cikin sauki zai zama madauwami, sannan ya lalata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila-Masar a 1979, kuma hakan zai lalata rayuwar Falasdinawa da ke tirjiya: neman hakkin kafa kasarsu. Alkahira ta sha zama a kan gaba wajen ganin an tsagaita wuta, kuma ta zama mai tantama kan tabbacin Isra'ila dangane da kwararar masu gudun hijira zuwa kan iyaka. A farkon wannan watan, Masar ta yi amfani da kyakkyawar alakarta da Amurka, Isra'ila da Qatar wajen ganin na dawo an ci gaba da tattaunawa samar da zaman lafiya. Duk da cewa ba a cimma da mai ido ba a wannan yunkuri, yadda Masar ke matsa lamba wajen ganin an sulhunta, na kawar da tunanin tana goyon bayan tirsasawa mutane barin matsugunansu. Idan har manufar da ake da ita, ita ce a tattara wadanda aka raba da gidajensu a kan iyakar, to ai ba a yi tunani ba ga Masar a ce wai tana adawa da hatsarin raba mutane da matsugunansu ta karfi da yaji, sannan ta yi watsi da hare-hare ta kasa na Isra'ila. A wannan makon a Kotun Hukunta Manyan laifuka ta Kasa da Kasa, Masar ta yi sauri wajen sukar manufofin isra'ila na raba mutane da dama da matsugunansu, hukunta kowa da kowa, da kai hare-hare ba tare da tantancewa ba a kan Falasdinawa, inda take bayar da mislai kan shirin kai hari rafah da alama ta karara game da tirsasa gudun hijira. Wadannan abubuwa kira ne ga hasashen da ake yi; cewa Masar na gina wani yanki na "zaman lafiya" ga Falasdinawa a bangaren iyakarta. Yin wannan gini na nufin ta amince da sakamakon da zai biyo bayan hare-haren da Isra'ila za ta kai Rafah. Masar ta kasance mai nuna adawa a bayyana game da tirsasawa Falasdinawa gudun hijira, kuma ta ki yarda ta daina kira ga Isra'ila kan kar ta kai hare-hare Rafah. Duk wannan na bayyana gaskiya game da matsayar Masar da zsrgin da ake yi mata kan ta yarda da mai zai je ya komo bayan Isra'ila ta kai hare-hare Rafah. Wannan matakin gusawa ne a matsayar Masar kan gargadinda ta sha yi wa jami'an kasashen Yamma da suka hada da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, cewa tirsasawa 'yan yankin Gaza gudun hijira zuwa Sinai ba abu ne da za a amince da shi ba. Haka kuma, Alkahira ta nuna ba ta amince da tabbacin da isra'ila ta bayar na adawa da tirsasa gudun hijira. A 'yan kwanakin nan, Netanyahu na ta ƙara ɗaga murya wajen kiran da a fara kai hare-hare ta kasa a Rafah, ya bijirewa matsin lambar kasashen duniya, yana ta kokarin jan ra'ayin Amurka kan cewar za su tabbatar da ba a cutar da fararen hula ba a yankin. Da yake magana da Rueters, wani jami'in taron isra'ila ya bayyana cewa ba za a bar Falasdinawa su dawo arewacin Falasdinu, yana cin karo da matsayin gwamnatin Tel Aviv, tare da kalubalantar yiwuwar kai kayan taimako da agaji zuwa yankin da ke karkashin mamaya. Tun kafin hare-haren Isra'ila a Gaza, tuni aka saka shingaye a kan iyakokin Masar tare da samar da waje mai kama da na fakewa. Wannan gini da ake yi ya gabaci wannan rikici, da wahala ka alakanta cigaban yankunan kan iyakar a matsayin wani martani ga yiwuwar samuwar kwararar 'yan gudun hijirar Falasdin daga Rafah zuwa iyakar. Idan aka yi duba ga dukkan wannan, Masar ta zama mai adawa ga tirsasawa Falasdinawa barin matsugunansu, kuma ta hau dokin naki wajen daina kira ga isra'ila da ta guji kai hare-hare Rafah. Duk wannan na watsi da zarge-zargen Masar na shiryawa sakamakon hare-haren da Isra'ila ke shirin kai wa Rafah. Wanda ya rubuta wannan makala Hannan Hussain, kwararre ne kan harkokin kasa da kasa kuma marubucin litattafai. Malamin Fulbright ne kan tsaron Kasa da Kasa a Jami'ar Maryland, kuma ya taba zama mai bayar da shawara fa Cibiyar New Lines ta Sanin Makamar Aiki da Tsare-Tsare Tafiyar da Gwamnati da ke Washinton. An buga ayyukan Hussain a manyan mjallu na duniya irin su Carnegie Endowment for International Peace, Georgetown Journal of International Affairs, da Express Tribune. Togaciya : Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra'ayi ko manufofin TRT Afirka ba.