An haifi Maria Branyas Morera a San Francisco a cikin 1907 a cikin zuri'ar Catalan. Maria Branyas Morera, matar da ta fi tsufa a duniya, ta yi bikin cika shekaru 117 da haihuwa a yankin Catalonia na kasar Spain. “Tsufa wani nau'in ibada ne. "Ka rasa jin ka, amma a lokacin ne ma kake ji sosai saboda kuna jin yadda rayuwa ke kasancewara, ba hayaniya ba… Sanin cewa za ka mutu na sa ka sake gane muhimmancin rayuwa," ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, tana ambato wata magana da babban malamin ɗariƙar Katolika Pedro Casaldaliga. . Kundin bajinta na Guinness Book of World Records ya ayyana ta a matsayin wadda ta fi kowa tsufa a duniya a watan Janairun 2023, bayan da ɗaya matar da ta fi kowa tsufa ƴar Faransa Lucile Randon ta mutu tana da shekara 118. An haife ta a San Francisco a cikin 1907 a zuri'ar Catalan, ta koma zama tare da danginta a Spain lokacin tana da shekaru takwas. A lokacin tafiyar ta Atlantika, ta zama kurma a kunne ɗaya kuma mahaifinta ya mutu saboda tarin fuka.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Maria Morera: Wacce ta fi kowa tsufa a duniya tana murnar cikarta shekara 117
An haifi Maria Branyas Morera a San Francisco a cikin 1907 a cikin zuri'ar Catalan. Maria Branyas Morera, matar da ta fi tsufa a duniya, ta yi bikin cika shekaru 117 da haihuwa a yankin Catalonia na kasar Spain. “Tsufa wani nau'in ibada ne. "Ka rasa jin ka, amma a lokacin ne ma kake ji sosai sabo...

At a glance