Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Manyan ‘yan siyasar Nijeriya na kokawa kan matsalar lantarki a arewacin ƙasar

Bayan shafe kwanaki ana fama da rashin wutar lantarki a arewacin Nijeriya, tuni wasu daga cikin manyan 'yan siyasa na Nijeriya irin su Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso suka soma ƙorafi dangane da lamarin. Yayin da aka shafe kusan kwana takwas ana fama da matsalar wutar lantarki a arewacin Nijeri...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:17
Manyan ‘yan siyasar Nijeriya na kokawa kan matsalar lantarki a arewacin ƙasar
En bref

Bayan shafe kwanaki ana fama da rashin wutar lantarki a arewacin Nijeriya, tuni wasu daga cikin manyan 'yan siyasa na Nijeriya irin su Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso suka soma ƙorafi dangane da lamarin. Yayin da aka shafe kusan kwana takwas ana fama da matsalar wutar lantarki a arewacin Nijeri...

Bayan shafe kwanaki ana fama da rashin wutar lantarki a arewacin Nijeriya, tuni wasu daga cikin manyan 'yan siyasa na Nijeriya irin su Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso suka soma ƙorafi dangane da lamarin. Yayin da aka shafe kusan kwana takwas ana fama da matsalar wutar lantarki a arewacin Nijeriya, tuni wasu daga cikin ‘yan siyasar ƙasar suka soma ƙorafi dangane da halin da aka shiga. Kamfanin da ke dakon wutar lantarki a ƙasar wato TCN ya ce an samu ɗaukewar wutar lantarki a yankin ne saboda lalata babban layin wutar lantarki da ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna da wasu ’yan bindiga suka yi, wanda shi ne yake bai wa yankin arewacin kasar wutar lantarki. A wata sanarwa da tsohon shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya fitar a shafinsa na X, ya ce matsalar wutar lantarki a Nijeriya babbar abin damuwa ce. The electricity power crisis in Nigeria continues to be a matter of immense concern. In particular reference is the situations in both the Southeast and the entire states of the Northwest and Northeast that have been in complete blackouts in the past three weeks. Every… — Atiku Abubakar (@atiku) October 26, 2024 “Duk ma’aikatar gwamnati da ke da alhakin shawo kan matsalar dole ne ta yi gaggawar shiga tsakani tare da mayar da wutar lantarki a yankunan da ke cikin mawuyacin hali,” in ji Atiku. Haka kuma Atikun ya yi kira kan a bayar da ƙwarin gwiwa ga ‘yan kasuwa da su zuba jari ta ɓangaren samar da wutar lantarki. Shi ma tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a Jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da wannan batu. “Wani abin takaici ne yadda a yau wasu sassa na Arewacin Nijeriya suka shiga duhu sakamakon barnar da aka yi a kan muhimmin layin wutar lantarki na Shiroro zuwa Kaduna mai karfin 330kV da ke samar wa jihohin Kano da Kaduna da kuma wani layin da ke samar da Bauchi da Gombe da sauran sassan arewa maso gabas. It is very disheartening that many parts of Northern Nigeria are in total darkness today due to vandalism on the important 330kV Shiroro-Kaduna power line that supplies the states of Kano and Kaduna and another line that supplies Bauchi, Gombe and other parts of the northeast.… — Rabiu Musa Kwankwaso (@KwankwasoRM) October 28, 2024 “Wannan lamari dai ya kara ta’azzara ne sakamakon tsadar man fetur da dizal a Nijeriya, lamarin da ya kara jefa gidaje cikin duhu tare da tilasta rufe masana'antu,” in ji Kwankwason. Tun bayan faruwar matsalar ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu da iyalai da sauran harkokin yau da kullum a arewacin kasar sun shiga halin-ni-’yasu kasancewar yadda abubuwa da dama suka dogara kan wutar lantarki a wannan zamani. A baya idan aka samu daukewar wutar lantarki na tsawon lokaci a kasar, wasu ’yan kasar musamman masu sana’o’i hannu kamar teloli da masu aski da sauransu sukan sayi man fetur ne don su ci gaba da sana’o’insu kafin a samu wutar lantarkin. Sai dai a wannan lokaci hakan yana yi wa masu sana’o’i wahala kasancewar man fetur kansa shi ma farashinsa ya yi sama sosai, inda yanzu ake sayar da lita daya a kan akalla naira 1,000.