Ministan Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jagoranci manyan jami'an gwamnatin ƙasar wajen tattaunawa da gwamnatin sojin Nijar inda za a taimaka mata da na'urorin tsaro da leƙen asiri, inda ya nuna yadda Ankara ke taimaka wa Somalia a yaƙi da ta'addanci. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna da gwamnatin Nijar kan yaƙi da ta'addanci a ziyarar da ya kai ƙasar, yana mai cewa ta'addanci "shi ne babban abin da ke haddasa rashin zaman lafiya a yankin Sahel." "Mun tattauna kan abubuwan da suka kamata a yi a fannin ci gaban ayyukan tsaro da leƙen asiri a fafutukar yaƙi da ta'addanci a Nijar, kamar yadda muka yi a Somalia. Kazalika mun tattauna matakan da za mu ɗauka wajen yaƙi da ta'addanci, wanda shi ne babban abin da ke haifar da rashin zaman lafiya a yankin Sahel," in ji Fidan a hirar da manema labara a Yamai, babban birnin Nijar. Ministan Tsaron Ƙasa na Turkiyya Yasar Guler, Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa Alparslan Bayraktar, da Shugaban Hukumar Leƙen Asirin Ƙasa Ibrahim Kalin da sauran manyan jami'an gwamnatin ƙasar suna cikin mahalarta taron manema labaran. Fidan ya ce Turkiyya tana da ofisoshin jakadanci 44 a cikin ƙasashe 54 na Afirka, yana mai cewa: "Dangantakar da muke da ita da nahiyar Afirka tana samun ci gaba kuma tana ƙara yauƙi a kowace rana. Haɗin-gwiwar da muke da da ƙasashen Afirka a fannin diflomasiyya, tattalin arziki, harkokin kuɗi, tsaro, ilimi da kiwon lafiya na ƙara ƙarfi." Fidan ya jaddada tarihin alaƙar Turkiyya da Nijar inda ya ce ta samo asali ne tun zamanin Daular Usmaniyya kuma a shekarun baya bayan nan jami'an gwamnatin Turkiyya suna ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa wannan dangantaka. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya halarci taron ƙungiyar haɗin gwiwa a Nijar Ya ƙara da cewa, "A yayin da muke ci gaba da yauƙaƙa dangantaka da Afirka, muna kuma aiwatar da wasu tsare da za su mayar da hankali wajen amfana da kuma ci gaban 'yan'uwanmu mutanen karkara. Zaman lafiya da tsaron Afirka na cikin manyan abubuwan da muka sanya a gaba. Kamar yadda aka sani, matsalar rashin tsaro da ta'addanci a yankin Sahel tana ci gaba da yin ƙamari".
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Manyan jami'an gwamnatin Turkiyya sun tattauna kan yaƙi da ta'addanci a ziyarar da suka kai Nijar
Ministan Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jagoranci manyan jami'an gwamnatin ƙasar wajen tattaunawa da gwamnatin sojin Nijar inda za a taimaka mata da na'urorin tsaro da leƙen asiri, inda ya nuna yadda Ankara ke taimaka wa Somalia a yaƙi da ta'addanci. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya...

A taƙaice
Ministan Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jagoranci manyan jami'an gwamnatin ƙasar wajen tattaunawa da gwamnatin sojin Nijar inda za a taimaka mata da na'urorin tsaro da leƙen asiri, inda ya nuna yadda Ankara ke taimaka wa Somalia a yaƙi da ta'addanci. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya...
