Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD

Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko. Hukumar da ke kula da harkar noman koko ta ƙasar Ghana (COCOBOD) ta ce manoman koko a ƙasar sun fi takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire samun...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:17
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
Kwa muhtasari

Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko. Hukumar da ke kula da harkar noman koko ta ƙasar Ghana (COCOBOD) ta ce manoman koko a ƙasar sun fi takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire samun...

Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko. Hukumar da ke kula da harkar noman koko ta ƙasar Ghana (COCOBOD) ta ce manoman koko a ƙasar sun fi takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire samun farashi mai kyau, kuma duk labarin da ya saɓa wa hakan ba gaskiya ba ne. Hukumar ta bayyana jajircewarta wajen tabbatar da jin daɗin manoma da ƙarfafa ɗorewar fannin noman koko da kuma tabbatar da shugabancin Ghana a fannin koko. Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba a babban birnin ƙasar Accra ta yi ƙarin haske game da wasu rahotanni da ra’ayoyin jama’ar ƙasar da ke nuna cewa farashin koko daga bakin gona a Ghana bai kai farashin koko ba a Côte d’Ivoire. Sanarwar ta ce alƙaluman kasuwa na yanzu da kuma sharhi na masu zaman kansu sun nuna cewa manoman koko na ƙasar Ghana suna samun kuɗi fiye da takwarorinsu na ƙasar Côte d’Ivoire. Sanarwar ta ce, rahoton watan Agustan shekarar 2025 na cibiyar da ke sa ido kan saye da sayar da kayayyaki ya nuna cewa farashin da ake sayar da kokon Ghana ya tsaya a kan ¢3,228.75 kan ko wane buhu mau nauyin kilogiram 64 na koko (kwatankwacin ¢51,660 ga ko wane tan ko kuma $5,040.00/ ga ko wane tan).