Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Manchester City ta samu kudin shigar da ya kai £712.8m a shekarar 2022/23

Kungiyar Manchester City ta fitar da rahotonta na shekara-shekara na 2022/2023 wanda ya nuna gagarumar ribar da ta samu cikin shekaru biyu. Manchester City ta fitar da rahoton kudaden shigar da ta samu a shekarar 2022/2023 wanda ya kai fam miliyan 712.8. Hakan ya nuna cewa kungiyar ta samu karin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:17
Manchester City ta samu kudin shigar da ya kai £712.8m a shekarar 2022/23
At a glance

Kungiyar Manchester City ta fitar da rahotonta na shekara-shekara na 2022/2023 wanda ya nuna gagarumar ribar da ta samu cikin shekaru biyu. Manchester City ta fitar da rahoton kudaden shigar da ta samu a shekarar 2022/2023 wanda ya kai fam miliyan 712.8. Hakan ya nuna cewa kungiyar ta samu karin...

Kungiyar Manchester City ta fitar da rahotonta na shekara-shekara na 2022/2023 wanda ya nuna gagarumar ribar da ta samu cikin shekaru biyu. Manchester City ta fitar da rahoton kudaden shigar da ta samu a shekarar 2022/2023 wanda ya kai fam miliyan 712.8. Hakan ya nuna cewa kungiyar ta samu karin £99.8m a kan kudin shigar da ta samu a bara sannan ya zarta £648.4m da kishiyarta Manchester United ta samu a shekarar kudi ta 2022/2023 . Kazalika City ta samu ribar £80.4m , wato kari kan £41.7m da ta samu a bara. Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ce a shekarar da ta lashe kofuna uku, wato Kufun Gasar Firmiya da na FA da kuma na Zakarun Turai, inda ta kasance ta biyu da ta dauki kofuna uku a kakar wasa daya bayan Manchester United wadda ta yi irin wanna bajinta a 1999. Rahoton ya nuna muhimman hanyoyin uku da ke samar wa kungiyar kudaden shiga da suka hada da kasuwancinta da watsa shirye-shirye da kuma tsare-tsarenta na gudanarwa.