Kayan yaƙin sun haɗa da jirgi mara matuƙi mai suna AKINCI, wanda kamfanin Turkiyya, Baykar, ya ƙera da aka fi sani da TB2. Ƙasar Mali ta sayi sabbin kayan yaƙi daga Turkiyya, ciki har da jirage marasa matuƙa, domin ƙarfafa yaƙin da take yi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda. Shugaban mulkin sojin Mali, Janar Assimi Goita, ya miƙa sabbin kayan yaƙin ga Rundunar Sojojin Mali (FAMa) a Bamako ranar Talata, ta hannun Ma'aikatar Tsaro da 'Yan Mazan-Jiya, a cewar gidan talbijin na ƙasar. Waɗannan kayan yaƙi na zamani za su ƙarfafa fafutukar da ƙasar take yi wajen kawar da 'yan ta'adda tare da inganta tsaronta, a cewarsa . Kayan yaƙin sun haɗa da jirgi mara matuƙi mai suna AKINCI, wanda kamfanin Turkiyya, Baykar, ya ƙera da aka fi sani da TB2. Bayar da fifiko Ministan Tsaron Mali, Janar Sadio Camara, ya yi maraba da wannan ƙoƙari, inda ya ce: "Amfani da kasafin kuɗi waje sayen waɗannan sabbin jirage zai buɗe mana sabuwar hanya. Za su taimaka mana wajen tsaron ƙasa tare da kawar da 'yan ta'adda." "Hukumomin Mali sun bayar da da fifiko wurin dawo da tsaron ƙasar sakamakon ci gaba da suke yi da sauraren buƙatun al'umma," in ji Janar Camara. Ministan Tsaron ya ƙarfafa gwiwar dakarun tsaro domin su yi aiki da waɗannan kayan yaƙi yadda ya kamata wajen biyan buƙatun al'ummar Mali waɗanda ke fama da hare-haren Abzinawa 'yan a-aware da sauran ƙungiyoyin 'yan ta'adda.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Mali ta karɓi sabbin kayan yaƙin da ta sayo daga Turkiyya domin murƙushe 'yan ta'adda
Kayan yaƙin sun haɗa da jirgi mara matuƙi mai suna AKINCI, wanda kamfanin Turkiyya, Baykar, ya ƙera da aka fi sani da TB2. Ƙasar Mali ta sayi sabbin kayan yaƙi daga Turkiyya, ciki har da jirage marasa matuƙa, domin ƙarfafa yaƙin da take yi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda. Shugaban mulkin sojin Mali, J...

Em resumo
Kayan yaƙin sun haɗa da jirgi mara matuƙi mai suna AKINCI, wanda kamfanin Turkiyya, Baykar, ya ƙera da aka fi sani da TB2. Ƙasar Mali ta sayi sabbin kayan yaƙi daga Turkiyya, ciki har da jirage marasa matuƙa, domin ƙarfafa yaƙin da take yi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda. Shugaban mulkin sojin Mali, J...
