Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Majalisar Dokokin Kano ta soke Masarautu 5 da Gwamnatin Ganduje ta ƙirƙira

Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta soke sarakuna biyar da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta naɗa. Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis ɗin nan. A jawabin da ya gabatar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Lawal Hussaini, ya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:17
Majalisar Dokokin Kano ta soke Masarautu 5 da Gwamnatin Ganduje ta ƙirƙira
A taƙaice

Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta soke sarakuna biyar da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta naɗa. Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis ɗin nan. A jawabin da ya gabatar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Lawal Hussaini, ya...

Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta soke sarakuna biyar da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta naɗa. Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi a ranar Alhamis ɗin nan. A jawabin da ya gabatar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Lawal Hussaini, ya ce majalisar ta soke dukkan "masarauti biyar da aka ƙirƙira inda za a koma tsarin Masarauta guda ɗaya kamar yadda yake a baya." Masarautun da aka soke su ne: Birnin Kano, Gaya, Rano, Bichi da Ƙaraye. A shekarar 2019 dai aka yi wa dokar masarautu a jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar.