Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci hukumomin yaƙi da rashawa su bincike El-Rufai

Rahoton binciken da aka gabatar a gaban majalisar ya zargi El-Rufai da wasu manyan muƙarraban gwamnatinsa da cin amanar aiki da halasta kuɗin haram da cin bashi ba bisa ƙa'ida ba. Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta buƙaci hukumomin da ke yaƙi da rashawa su binciki tsohon gwamnan jihar Nasir El Ruf...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:17
Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci hukumomin yaƙi da rashawa su bincike El-Rufai
A taƙaice

Rahoton binciken da aka gabatar a gaban majalisar ya zargi El-Rufai da wasu manyan muƙarraban gwamnatinsa da cin amanar aiki da halasta kuɗin haram da cin bashi ba bisa ƙa'ida ba. Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta buƙaci hukumomin da ke yaƙi da rashawa su binciki tsohon gwamnan jihar Nasir El Ruf...

Rahoton binciken da aka gabatar a gaban majalisar ya zargi El-Rufai da wasu manyan muƙarraban gwamnatinsa da cin amanar aiki da halasta kuɗin haram da cin bashi ba bisa ƙa'ida ba. Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta buƙaci hukumomin da ke yaƙi da rashawa su binciki tsohon gwamnan jihar Nasir El Rufai da wasu muƙarraban gwamnatinsa kan zargin cin amanar aiki da halasta kuɗin haram. Wannan na zuwa ne bayan bincike na musamman da wani kwamitin majalisar ya gudanar ƙarƙashin jagorancin Henry Zacharia. A cewar rahoton da Zacharia ya gabatar a ranar Laraba, yawancin bashin kuɗin da aka samu a karkashin gwamnatin El-Rufai, ba a yi amfani da su yadda suka dace, kuma a wasu lokuta, ba a bi ka’idojin da suka dace wajen samun bashin ba. Don haka kwamitin ya bayar da shawara ga hukumomin yaƙi da rashawa su gudanar da bincike da gurfanar da tsohon gwamnan da wasu jami’an gwamnatin kan zargin amfani da mukami domin bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’ida ba, da karkatar da kudaden jama’a, da kuma kudade.