Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Majalisar Dattawa ta amince da aikawa da sakamakon zaɓe ta intanet

Za a fara da na’ura, sai takarda idan intanet ya samu matsala Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aikawa da sakamakon zaɓe kai-tsaye ta intanet a cikin ƙudurin gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2022, bayan zaman gaggawa da ta gudanar a ranar Talata sakamakon ce-ce-ku-ce da batun ya haifar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:17
Majalisar Dattawa ta amince da aikawa da sakamakon zaɓe ta intanet
En bref

Za a fara da na’ura, sai takarda idan intanet ya samu matsala Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aikawa da sakamakon zaɓe kai-tsaye ta intanet a cikin ƙudurin gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2022, bayan zaman gaggawa da ta gudanar a ranar Talata sakamakon ce-ce-ku-ce da batun ya haifar...

Za a fara da na’ura, sai takarda idan intanet ya samu matsala Majalisar Dattijan Nijeriya ta amince da tsarin aikawa da sakamakon zaɓe kai-tsaye ta intanet a cikin ƙudurin gyaran dokar zaɓe ta shekarar 2022, bayan zaman gaggawa da ta gudanar a ranar Talata sakamakon ce-ce-ku-ce da batun ya haifar a ƙasar. TRT Hausa Tun da fari, Majalisar Wakilai ta yarda a wajabta tsarin aikawa da sakamakon ta na’ura, yayin da Majalisar Dattawa ta dage cewa tsarin ya kasance zaɓi ne ba dole ba, abin da ya haifar da sabani tsakanin majalisun biyu. TRT Hausa Majalisar Dattawa ta bayyana cewa aika sakamakon kai-tsaye ta na’ura zai kasance mataki na farko, amma idan aka samu matsalar intanet, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta koma amfani da tsarin rubuta sakamakon a takarda kamar yadda aka saba. TRT Hausa Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da ƙudurin, yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da amincewa da shi bayan samun goyon bayan sauran ‘yan majalisar. TRT Hausa Haka kuma, Majalisar ta kafa kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki tare da Majalisar Wakilai wajen daidaita matsayar dokar, biyo bayan zanga-zangar da ƙungiyoyin fararen-hula da jam’iyyun hamayya suka yi a harabar majalisar kan ƙin wajabta aikawa da sakamakon zaɓe ta na’ura. TRT Hausa