Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a yi karatu na biyu ga ƙudurin dokar haraji

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi karatun farko ga dokar haraji ta ƙasar, inda a halin yanzu ta amince a yi karatu na biyu. Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi karatun farko ga dokar haraji ta ƙasar, inda a halin yanzu ta amince a yi karatu na biyu. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya aike wa majal...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:17
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince a yi karatu na biyu ga ƙudurin dokar haraji
A taƙaice

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi karatun farko ga dokar haraji ta ƙasar, inda a halin yanzu ta amince a yi karatu na biyu. Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi karatun farko ga dokar haraji ta ƙasar, inda a halin yanzu ta amince a yi karatu na biyu. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya aike wa majal...

Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi karatun farko ga dokar haraji ta ƙasar, inda a halin yanzu ta amince a yi karatu na biyu. Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi karatun farko ga dokar haraji ta ƙasar, inda a halin yanzu ta amince a yi karatu na biyu. Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya aike wa majalisar da ƙudurin dokar harajin ƙasar wanda ya jawo ce-ce-ku-ce. Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da ƙudurin a gaban majalisar inda sanatoci suka yi muhawara a kansa. A ranar 3 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu Bola ya miƙa wa majalisar dokokin ƙasar wasu ƙudurorin gyara dokar haraji guda huɗu domin amincewa da su, sai dai sun jawo ce-ce-ku-ce da suka musamman daga arewacin ƙasar. Matakin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce inda gwamnonin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki suka yi fatali da gyaran dokar harajin.