Tshon Shugaban na Ghana John Mahama ya samu kusan 57% na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasar na ranar 7 ga Disamba, inda ya samu nasar a kan Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia. An ayyana tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da yammacin Litinin, bayan da masu kaɗa kuri'a suka nuna fushinsu kan yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin ƙasar. Tsohon shugaban ƙasar tsakanin 2012 zuwa 2017, Mahama, mai shekaru 65, ya samu kuri'u miliyan 6.3, wato kashi 56.5% na ƙuri'un da aka kaƙa, in ji hukumar zaɓen ƙasar. Babban abokin hamayyar Mahama, Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye a ranar Lahadi. Bawumia ya samu kuri'u miliyan 4.6, wato kashi 41%. Yawan ƙuri’un da aka kaɗa a mazaɓu 267 ya kai kashi 60.9%, in ji Shugabar Hukumar Zaɓen Ƙasar Jean Mensa. Mensa ta ƙara da cewa duk da cewa ana ci gaba da ƙidayar kuri'u a mazabu tara, amma hakan ba zai sauya sakamakon ƙarshe ba. ‘Nasarar’ a bayyane Bayan da Bawumia ya amince da shan kaye a ranar Lahadin da ta gabata, magoya bayan dan takarar na hamayya sun gudanar da bukukuwa a sassan kasar ciki har da babban birnin kasar. Sanye da tufafi masu launin fari, kore, ja da baki na jam’iyyar adawa, mata da matasa sun yi ta raye-raye suna kade-kade da busa kaho a kan tituna da kuma hedikwatar jam’iyyar ta kasa. An dai gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tsadar rayuwa mafi muni a cikin tsararraki. Ana yi wa zaben kallon tamkar wani gwaji ne na dimokuradiyya a yankin da tashe-tashen hankula da juyin mulki suka girgiza. Kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta ce gaba ɗaya zaben ya gudana cikin lumana, wanda ke ci gaba da gudana a Ghana. Jam'iyyar Mahama ta lashe rinjayen 'yan majalisa Bawumia dai ya tsaya takarar ne a tutar jam'iyyar New Patriotic Party, ko NPP mai mulki, wacce ta yi ta fama da matsalar tattalin arziki a karkashin shugaba mai barin gado Nana Akufo-Addo. Jam'iyyar Mahama ta National Democratic Congress ita ma ta samu rinjaye a majalisar, in ji shi. Ana kallon nasarar da Mahama ya samu a matsayin sabon salo na zabuka a duniya, wanda ke fifita jam'iyyun adawa fiye da masu mulki, daga Amurka zuwa kasashen Turai - irin su Birtaniya da Faransa - da kuma Afirka ta Kudu. ‘Nasaba da tattalin arziki' Kamar dai a yawancin zaɓuɓɓukan da ake yi a Ƙasashen da shugaba mai ci ya sha kaye, kuri’un da aka kaɗa a Ghana na nuni da cewa jama’a sun bayyana rashin amincewarsu da gwamnatin da jama’a suka dawo daga rakiyarta, in ji Seidu Alidu, shugaban sashen nazarin kimiyyar siyasa na jami’ar Legon ta Ghana. "Ina ganin yana da nasaba da tattalin arziki, wanda galibi shi ne batun da ya fi damun kowane ɗan Ghana," in ji Alidu. “Lokacin da mutane suka zaɓe ka, suna buƙatar ka yi musu wasu abubuwa. Sai dai kuma ya shafi salon mulkin ne (saboda) hatta a sauran ƙasashen da ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki, gwamnatoci suna fitowa su gaya wa jama’a gaskiya, suna gaya musu hakikanin abin da ke faruwa, da kuma matakan da suka ɗauka wajen tafiyar da shi,” kamar yadda ya bayyana.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Mahama ya lashe zaɓen shugaban gahna da 57% na ƙuri'un da aka kaɗa: Hukumar Zaɓe
Tshon Shugaban na Ghana John Mahama ya samu kusan 57% na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasar na ranar 7 ga Disamba, inda ya samu nasar a kan Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia. An ayyana tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban k...

A taƙaice
Tshon Shugaban na Ghana John Mahama ya samu kusan 57% na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasar na ranar 7 ga Disamba, inda ya samu nasar a kan Mataimakin Shugaban Ƙasa Mahamudu Bawumia. An ayyana tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban k...
