Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Nijar Ta Gabatar Da Sabbin Dabarun Inganta Fannin Man Fetur

Tsarin ya ƙunshi inganta zuba jari, shugabanci da bayyana gaskiya Ministan albarkatun man Nijar , Hamadou Tini, ya gabatar da dabarun inganta fannin man fetur na ma’aikatarsa a ranar Talata a gaban mambobin Majalisar Ceto Ƙasa (CNSP) da sauran masu ruwa da tsaki. ANP Kamfanin dillancin labaran ƙa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:17
Nijar Ta Gabatar Da Sabbin Dabarun Inganta Fannin Man Fetur
De un vistazo

Tsarin ya ƙunshi inganta zuba jari, shugabanci da bayyana gaskiya Ministan albarkatun man Nijar , Hamadou Tini, ya gabatar da dabarun inganta fannin man fetur na ma’aikatarsa a ranar Talata a gaban mambobin Majalisar Ceto Ƙasa (CNSP) da sauran masu ruwa da tsaki. ANP Kamfanin dillancin labaran ƙa...

Tsarin ya ƙunshi inganta zuba jari, shugabanci da bayyana gaskiya Ministan albarkatun man Nijar , Hamadou Tini, ya gabatar da dabarun inganta fannin man fetur na ma’aikatarsa a ranar Talata a gaban mambobin Majalisar Ceto Ƙasa (CNSP) da sauran masu ruwa da tsaki. ANP Kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP, ya ruwaito cewa tsarin ya ƙunshi ɓangarori bakwai, ciki har da inganta zuba jari a bincike da hako mai, da ƙarfafa jagoranci da inganta tsarin gudanarwa a fannin. ANP Dabarun sun kuma haɗa da samar da wata hukuma mai zaman kanta da za ta sa ido kan ɓangaren man Nijar, wadda za ta kula da harkokin ɗanyen mai da rarraba tacaccen mai tare da tabbatar da bin doka a fannin tattalin arziƙi. ANP Sauran muhimman ɓangarorin sun haɗa da ƙarfafa kamfanonin cikin gida, haɓaka ƙwarewar ‘yan ƙasa, buɗe ƙofa a hankali ga ƙwarewar ƙetare, da kuma kula da muhalli da tasirin zamantakewa tare da tabbatar da gaskiya da bayyana bayanai ga jama’a. ANP A jawabinsa, Ministan ya jaddada cewa tsarin ya dace da tsare-tsaren sake fasalin ƙasar da ke ba da fifiko ga ‘yancin tattalin arziki, shugabanci na gari, gaskiya da kuma amfani mai kyau da albarkatun ƙasa. ANP Ya ƙara da cewa tsarin ya ƙunshi dabaru da umarnin aiki da ke da nufin ƙara gudunmawar fannin mai ga kuɗaɗen shigar ƙasa, inganta shugabanci da bayyana gaskiya, ƙara shigar ‘yan ƙasa a harkar, da tafiyar da fannin ta hanya mai ɗorewa. ANP