Romelu Lukaku na Napoli ya samu rauni a cinya yayin wasan sada-zumunta na share fagen gasar Serie A ta Italiya. Ɗan wasan Napoli, Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa yayin wasan sada-zumunta da Olympiacos, kafin fara gasar Serie A ta Italiya. Raunin zai tilasta masa tafiya jinyar watanni uku har zuwa Nuwamba, kamar yadda Napoli ta tabbatar a wata sanarwa. Sanarwar ta ce, "Sakamakon raunin da ya samu yayin wasa da Olympiacos, an yi wa Romelu Lukaku gwaje-gwaje a asibitin Pineta Grande Hospital, wanda ya bayyana babban rauni a ƙashin cinyarsa ta hagu. Ɗan wasan tuni ya fara samun kulawa kuma zai samu shawar likita kan tiyata." An yi wa ɗan wasan ɗan asalin Belgium gwajin likita a asibitin Pineta Grande Hospital, kuma rahotanni sun nuna ya samu babban rauni a ƙashin cinyarsa. Lukaku dai yana da babban tasiri a ƙungiyar Napoli a baya-bayan nan ƙarƙashin koci Antonio Conte, wanda a baya sun yi aiki tare a Inter.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Lukaku zai yi jinya har zuwa Nuwamba yayin da Napoli za ta fara kare kambin Serie A bana
Romelu Lukaku na Napoli ya samu rauni a cinya yayin wasan sada-zumunta na share fagen gasar Serie A ta Italiya. Ɗan wasan Napoli, Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa yayin wasan sada-zumunta da Olympiacos, kafin fara gasar Serie A ta Italiya. Raunin zai tilasta masa tafiya jinyar watanni uku h...
لمحة سريعة