Gwamnatin India ta yi kira ga likitoci da su dawo bakin aiki sannan ta kafa kwamiti don bayar da shawarwari kan yadda za a bayar da kariya ga ma'aikatan lafiya. Dubban ƙananan likitoci a India sun ƙi daina zanga-zangar da suke yi sakamakon fyaɗe da kashe abokiyar aikinsu, inda suka kawo cikas ga ayyukan asibiti kusan tsawon mako guda suna neman a samar da tsaro ga ma'aikatan lafiya da hukunta masu hannu kan lamarin. Likitoci a faɗin ƙasar sun ci gaba da zanga-zangar inda suka ƙi duba marasa lafiyar da ba sa buƙatar agajin gaggawa, saboda kisan abokiyar aikinsu mai shekara 31 bayan an yi mata fyaɗe a wani asibiti da ke birnin Kolkata na gabashin India. An kama wani ɗan sandan sa-kai da laifin kisanta tare da tuhumarsa. Mata masu fafutuka sun ce wannan lamari ya fito da yadda mata a India ke ci gaba da shan wahala saboda fyaɗe, duk da tsauraran dokokin da aka samar bayan fyaɗen da aka yi wa wata ɗaliba a 2012 tare da kisanta a cikin motar bas a New Delhi. Gwamnatin India ta yi kira ga likitoci da su koma bakin aiki sannan ta kafa kwamiti don bayar da shawarwari kan yadda za a bayar da kariya ga ma'aikatan lafiya. "Za mu ci gaba da ƙauce wa aiki da zaman-dirshan har sai an biya buƙatarmu," in ji Dr. Aniket Mahata, mai magana da yawun ƙananan likitoci a Kwalejin Magani da Asibitin R.G Kar, inda a nan ne lamarin ya faru. Domin nuna goyon baya ga likitocin, dubban magoya bayan manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa biyu na jihar Bengal ta Yamma sun yi tattaki a titunan Kolkata a yammacin Lahadin da ta gabata suna cewa "Muna so a yi adalci". Ƙungiyar da ke wakiltar ƙananan likitocin a maƙociyar jihar Odisha, babban birnin New Delhi da jihar Gujarat ta yammacin ƙasar sun ce za su ci gaba da zanga-zangar.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Likitocin India sun ƙi dakatar da zanga-zanga saboda fyaɗe da kashe abokiyar aikinsu
Gwamnatin India ta yi kira ga likitoci da su dawo bakin aiki sannan ta kafa kwamiti don bayar da shawarwari kan yadda za a bayar da kariya ga ma'aikatan lafiya. Dubban ƙananan likitoci a India sun ƙi daina zanga-zangar da suke yi sakamakon fyaɗe da kashe abokiyar aikinsu, inda suka kawo cikas ga...

Gwamnatin India ta yi kira ga likitoci da su dawo bakin aiki sannan ta kafa kwamiti don bayar da shawarwari kan yadda za a bayar da kariya ga ma'aikatan lafiya. Dubban ƙananan likitoci a India sun ƙi daina zanga-zangar da suke yi sakamakon fyaɗe da kashe abokiyar aikinsu, inda suka kawo cikas ga...
