Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Libya da Turkiyya sun tattauna kan atisayen soji na haɗin-gwiwa

A yayin da ya kai ziyarar aiki Libya, Gurak ya miƙa saƙon shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ga Firaminista Dbeibeh inda ya jaddada daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin Libya. Firaministan Libya Abdulhamid Dbeibeh da Hafsan Hafsoshin sojojin ƙasa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:15
Libya da Turkiyya sun tattauna kan atisayen soji na haɗin-gwiwa
En bref

A yayin da ya kai ziyarar aiki Libya, Gurak ya miƙa saƙon shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ga Firaminista Dbeibeh inda ya jaddada daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin Libya. Firaministan Libya Abdulhamid Dbeibeh da Hafsan Hafsoshin sojojin ƙasa...

A yayin da ya kai ziyarar aiki Libya, Gurak ya miƙa saƙon shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ga Firaminista Dbeibeh inda ya jaddada daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin Libya. Firaministan Libya Abdulhamid Dbeibeh da Hafsan Hafsoshin sojojin ƙasa na Turkiyya Metin Gurak sun tattauna ranar Lahadi game da ayyukan haɗin-kai tsakanin hafsoshin sojojin ƙasa na ƙasashensu tare da gudanar da atisayen soji na haɗin-gwiwa. A yayin da ya kai ziyarar aiki Libya, Gurak ya miƙa saƙon shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ga Firaminista Dbeibeh inda ya jaddada daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin Libya. Ɓangarorin biyu sun tattauna kan haɗin-kai da shirye-shiryen bayar da horo tsakanin ma'aikatun tsaro da hafsoshin sojojinsu tare da gudanar da atisayen soji na haɗin-giwa. Jakadan Turkiyya a Libya Guven Begec da Hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Libya Muhammad Ali Ahmad al-Haddad da mataimakinsa Laftanar Janar Salah Al-Namroush na cikin waɗanda suka halarci taron. Tun da farko, Gurak ya gana da shugaban Majalisar Fadar shugaban ƙasar Libya, Mohamed al-Menfi, da Hafsan Hafsoshin sojojin Libya Al-Haddad sannan ya ziyarci Ofishin Jakadancin Turkyya a Tripoli.