Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar yin garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana gazawarsa wajen tunkarar al'amuran duniya da suka haɗa da na Gaza. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar yin garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana gazawarsa wajen tunkarar al'amuran duniya da suka haɗa da na Gaza. A rana ta biyu ta taron Ministocin Harkokin Wajen kasashen G20 a Brazil, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya halarci taron sake fasalin tsarin mulki na duniya a yau Alhamis, inda ya bayyana muhimmancin cibiyoyi masu inganci da kuma ingantattun hanyoyin gudanar da mulki a duniya don magance tashe-tashen hankula na yankuna a cikin sabon tsarin duniya na yau. Ya ce ya zama wajibi a fahimci buƙatar samun sauyin, kuma ya kamata a ba da fifiko wajen yin garambawul ga Kwamitin Tsaro, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya. Fidan ya ce Majalisar ta yi watsi da martabar tsarin MDD baki daya, kuma ana buƙatar “tsari mai inganci da tsarin dimokuraɗiyya” bisa ƙa’idojin dokokin ƙasa da ƙasa. Majiyoyin sun ce Fidan ya kuma lura cewa ya kamata tsarin hada-hadar kudi na ƙasa da ƙasa ya kasance "mai haɗo kowa da kowa bisa gaskiya da ƙa'ida kuma mai ɗorewa." Ya ce ya kamata cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa da bankunan ci gaban ƙasashe daban-daban su yi amfani da manufofin da suka dace da kasashe masu tasowa da wadanda ba su da ci gaba don cike giɓin da ke tsakanin ƙasashe masu tasowa. Idan ba haka ba, in ji Fidan, ba za a iya cimma burin ci gaba mai ɗorewa ba. Ya ƙara da cewa G20 na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen taimaka wa lamarin.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kwamitin Tsaro na MDD na buƙatar gyara: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar yin garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana gazawarsa wajen tunkarar al'amuran duniya da suka haɗa da na Gaza. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar yin garambawul ga Kwamiti...

لمحة سريعة
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar yin garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana gazawarsa wajen tunkarar al'amuran duniya da suka haɗa da na Gaza. Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar yin garambawul ga Kwamiti...
