A yau Talata ne shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Osifo ya sanar da janye yajin aikin a Abuja yayin wani taro da shugabannin kungiyoyin kwadagon. Kungiyoyin Ƙwadagon Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da aka fara jiya a kasar sakamakon neman gwamnati ta ƙara mafi karancin albashi da kuma adawa da ƙarin kudin wutar lantarki. A yau Talata ne shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Osifo ya sanar da janye yajin aikin a Abuja yayin wani taro da shugabannin kungiyoyin kwadagon. Tun da fari a ranar Litinin da yamma ƙungiyoyin ƙwadagon da wakilan gwamnatin tarayyar Nijeriya sun yi wata ganawa inda aka cimma matsaya hudu, ciki har da aniyar Shugaba Tinubu ta ƙara N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasa. Gidan talabijin na Channels ya rawaito Mista Osifo yana cewa "Bayan wani taron haɗin gwiwa na ƙungiyoyin ƙwadago na TUC/NLC sun amince da sassauta yajin aikin ne na tsawon mako guda ba tare da ɓata lokaci ba, Shugaban ƙungiyar ƙwadagon ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da bayanai a kan abubuwan da aka cim ma a wajen taron. Wasu labaran masu alaƙa Yajin aiki: Abu huɗu da NLC da gwamnatin Nijeriya suka cim ma Yadda yajin aikin NLC ya shafi jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kungiyoyin Kwadagon Nijeriya sun janye yajin aiki
A yau Talata ne shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Osifo ya sanar da janye yajin aikin a Abuja yayin wani taro da shugabannin kungiyoyin kwadagon. Kungiyoyin Ƙwadagon Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da aka fara jiya a kasar sakamakon neman gwamnati ta ƙara mafi karancin albash...

Bu haberde ne var?
A yau Talata ne shugaban kungiyar kwadago ta TUC Festus Osifo ya sanar da janye yajin aikin a Abuja yayin wani taro da shugabannin kungiyoyin kwadagon. Kungiyoyin Ƙwadagon Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da aka fara jiya a kasar sakamakon neman gwamnati ta ƙara mafi karancin albash...
