Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da 'makircin' Isra'ila kan Falasdinawa

Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kwato wa Falasdinawa hakkinsu Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah da ke Nijeriya ta yi Allaha yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya "ta dauki mataki kan zaluncin" da Isra'ila take yi wa Falasdinawa. Wata sanarwa da kungiyar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:14
Kungiyar Izala ta yi Allah wadai da 'makircin' Isra'ila kan Falasdinawa
A taƙaice

Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kwato wa Falasdinawa hakkinsu Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah da ke Nijeriya ta yi Allaha yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya "ta dauki mataki kan zaluncin" da Isra'ila take yi wa Falasdinawa. Wata sanarwa da kungiyar...

Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kwato wa Falasdinawa hakkinsu Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah da ke Nijeriya ta yi Allaha yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya "ta dauki mataki kan zaluncin" da Isra'ila take yi wa Falasdinawa. Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook ta ambato shugabanta Sheikh Abdullahi Bala Lau yana cewa ya kamata a bai wa Falasdinawa hakkinsu a lokacin da yake magana a wa'azin kasa da kungiyar ta gudanar a jihar Katsina a arewa maso yammacin Nijeriya. Shugaban ya ce Isra'ila tana kauce wa duk wani kudurin zaman lafiya da ake kawowa Majalisar Dinkin Duniya. Ya kara da cewa Majalisar Dinkin Duniya ba ta da amfani idan ba za ta iya kwato wa Falasdinawa hakkinsu ba. Sheikh Bala Lau ya yi kira ga al'ummar Musulmai da su yi addu'a Allah ya yi maganin masu zaluntar Falasdinawa.