Nijeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce kasa samar da danyen man fetur a nahiyar Afirka, ta samu kari a yawan danyen man da take hakowa a watan Disambar 2023, wanda ke nuni da samun karin kudin shiga daga albarkatun. Nijeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce kasa samar da danyen man fetur a nahiyar Afirka, ta samu kari a yawan danyen man da take hakowa a watan Disambar 2023, wanda ke nuni da samun karin kudin shiga daga albarkatun. Kasar ta dinga samar da ganga miliyan 1.34 na mai a kowace rana a cikin watan Disamban. Wannan dai ya zo ne a cewar majiyoyi daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC) a cikin rahotannin kasuwar mai na wata-wata (MOMRs), kamar yadda jaridar intanet ta Business Day ta rawaito. Yawan man da Nijeriya ke haƙowa ya ƙaru a wata da kashi 6.8 daga ganga miliyan 1.25 a watan Nuwamba 2023. Wani bincike ya nuna cewa an samu karin kashi 6.1 bisa 100 daga ganga miliyan 1.26 a watan Janairun 2023. Matsakaicin farashin danyen mai na Brent, ma'aunin man fetur na kasa da kasa da Nijeriya ke aunawa, ya tsaya kan dala 77.63 kan kowacce ganga a watan Disamba, a cewar cibiyar kididdiga ta Statista. Tun da farko, ƙaramin minista a ma’aikatar albarkatun man fetur Heineken Lokpobiri, ya ce an samu karuwar yawan danyen mai ne saboda gano tushen matsalar da gwamnati da ma’aikatan da ke kula da sassan suka yi.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Kudin shigar Nijeriya ya karu saboda yawan gangar fetur da take fitarwa ya kai miliyan 1.34
Nijeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce kasa samar da danyen man fetur a nahiyar Afirka, ta samu kari a yawan danyen man da take hakowa a watan Disambar 2023, wanda ke nuni da samun karin kudin shiga daga albarkatun. Nijeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce kasa samar da danyen man fetur...

Nijeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce kasa samar da danyen man fetur a nahiyar Afirka, ta samu kari a yawan danyen man da take hakowa a watan Disambar 2023, wanda ke nuni da samun karin kudin shiga daga albarkatun. Nijeriya wadda ita ce kasar da ta fi kowacce kasa samar da danyen man fetur...
