Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kotun Nijar ta cire wa Bazoum Mohamed rigar kariya

Hukumomin sojin Nijar suna zargin Bazoum da cin amanar ƙasa da ɗaukar nauyin 'yan ta'adda da kitsa tuggu ga ƙasar. Babbar kotun Jamhuriyar Nijar ta cire wa hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum rigar kariya, a wani mataki da ake gani zai bayar da ƙofa a tuhume shi tun bayan kifar da gwamnatin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:14
Kotun Nijar ta cire wa Bazoum Mohamed rigar kariya
De un vistazo

Hukumomin sojin Nijar suna zargin Bazoum da cin amanar ƙasa da ɗaukar nauyin 'yan ta'adda da kitsa tuggu ga ƙasar. Babbar kotun Jamhuriyar Nijar ta cire wa hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum rigar kariya, a wani mataki da ake gani zai bayar da ƙofa a tuhume shi tun bayan kifar da gwamnatin...

Hukumomin sojin Nijar suna zargin Bazoum da cin amanar ƙasa da ɗaukar nauyin 'yan ta'adda da kitsa tuggu ga ƙasar. Babbar kotun Jamhuriyar Nijar ta cire wa hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum rigar kariya, a wani mataki da ake gani zai bayar da ƙofa a tuhume shi tun bayan kifar da gwamnatinsa. "An bayar da umarni a cire wa Mohamed Bazoum rigar kariya," a cewar kotun wadda sojoji suka kafa a watan Nuwamba. Hukumomin sojin Nijar suna zargin Bazoum da cin amanar ƙasa da ɗaukar nauyin 'yan ta'adda da kitsa tuggu ga ƙasar. Bazoum na tsare a hannun hukumomin sojin Nijar tun da suka yi masa juyin mulki a watan Yulin shekarar 2023. A watan Agusta, sojojin ƙasar sun sanar da cewa za su tuhume da da laifukan "cin amanar ƙasa da yin ƙafar-ungulu ga tsaron Nijar".