Afirka ta Kudu ta nemi Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana cewa Isra’ila ta saɓa dokokin kisan kiyashi na majalisar, kana ta buƙaci a dakatar da yaƙin Isra'ila a Gaza da kudancin Rafah cikin gaggawa, tare da sauƙaƙa hanyoyin kai kayayyakin agaji. Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya za ta yanke hukunci a yau Juma’a kan buƙatar Afirka ta Kudu ta neman ta ba da umarnin dakatar da farmakin da sojojin Isra’ila ke kai wa a Gaza, inda Pretoria ta zargi Isra’ila da ''kisan kiyashi.'' Mahukunta a Pretoria sun buƙaci kotun ta MDD ta bayar da umarnin dakatar da yaƙin da Isra'ila ke yi cikin gaggawa, ciki har da yankin kudancin Rafah, tare da sauƙaƙa hanyoyin kai kayayyakin agaji. A nata ɓangaren, Isra'ila na son kotun ta yi watsi da buƙatar, tana mai cewa zargi ne da ba shi da tushe balle makama. A wani hukunci da ta yanke a watan Janairu, kotun ta umarci Isra'ila da ta yi dukkan mai yiwuwa wajen hana aikata laifin kisan kiyashi a Gaza sai dai ba ta bayar da umarni kan tsagaita wuta ba. Afirka ta Kudu ta ce harin da Isra'ila ta kai a Rafah na baya-bayan nan ya tsananta halin da ake ciki kuma ya kamata hakan ya tilasta wa kotun ta ba da sabbin umarnin gaggawa. Buƙatar kama Netanyahu Kotun Duniya ta ICJ za ta iya yanke hukunci kan taƙaddamar da ta taso tsakanin ƙasashe, da huruminta suna bisa ga tanadin doka sai dai ba ta da ƙarfin aiwatar da su kai-tsaye. Alƙalan kotun na iya amincewa da buƙatar Afirka ta Kudu ko su yi watsi da ita ko kuma su bayyana wani tsarin doka na daban. Hukuncin Kotun ICJ na zuwa ne a daidai gaɓar wata muhimmiyar buƙata da babban mai shigar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ya gabatar ta neman sammacin kama wasu manyan shugabannin Isra'ila. Mai gabatar da ƙara Karim Khan ya yi zargin cewa manyan shugabannin Isra'ila ciki har da Firaminista Benjamin Netanyahu sun aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil'adama. Keta yarjejeniyar kisan ƙare-dangi A wani zaman taron jin ra'ayin jama'a na kotun ICJ a makon da ya gabata, jakadan Afirka ta Kudu Vusimuzi Madonsela ya yi zargin cewa "kisan kiyashi da Isra'ila ke aikatawa ya tsananta kuma a yanzu ya kai wani sabon mataki mai ban tsoro". ''Duk da cewa buƙatar da ta taso a yanzu ta samo asali ne daga yanayin da ake ciki a Rafah, kana hare-haren da Isra'ila take yi a faɗin Gaza sun ƙara tsananta a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, lamarin da ke buƙatar kulawar wannan kotu,'' in ji shi. Afirka ta Kudu ta ce hanya ɗaya tilo da za a iya kai kayayyakin jinƙai don taƙaita raɗaɗin rikicin Gaza tana rufe sakamakon mamayar sojin Isra’ila.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kotun MDD za ta yanke hukunci a ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila
Afirka ta Kudu ta nemi Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana cewa Isra’ila ta saɓa dokokin kisan kiyashi na majalisar, kana ta buƙaci a dakatar da yaƙin Isra'ila a Gaza da kudancin Rafah cikin gaggawa, tare da sauƙaƙa hanyoyin kai kayayyakin agaji. Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya za ta yanke huku...

Afirka ta Kudu ta nemi Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana cewa Isra’ila ta saɓa dokokin kisan kiyashi na majalisar, kana ta buƙaci a dakatar da yaƙin Isra'ila a Gaza da kudancin Rafah cikin gaggawa, tare da sauƙaƙa hanyoyin kai kayayyakin agaji. Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya za ta yanke huku...
