Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano

Kotun Kolin ta soke nasarar da kotun sauraren kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka bai wa Nasiru Gawuna na APC, tana mai cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne halastaccen gwamnan jihar. Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan jihar Kano....

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:14
Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano
A taƙaice

Kotun Kolin ta soke nasarar da kotun sauraren kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka bai wa Nasiru Gawuna na APC, tana mai cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne halastaccen gwamnan jihar. Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan jihar Kano....

Kotun Kolin ta soke nasarar da kotun sauraren kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka bai wa Nasiru Gawuna na APC, tana mai cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne halastaccen gwamnan jihar. Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan jihar Kano. Kotun ta yanke hukuncin ne ranar Juma'a watanni goma bayan an gudanar da zaben gwamnan na jihar ta Kano mai cike da ce-ce-ku-ce. Gwamna Abba Gida-Gida ya garzaya Kotun Kolin ne bayan Kotun Daukaka Kara da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe sun ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC ne halastaccen gwamnan jihar. Kotun Kolin ta soke nasarar da kotun sauraren kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka bai wa Nasiru Gawuna na APC, tana mai cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne halastaccen gwamnan jihar. Jagoran alkalan Kotun, Mai Shari'a John Okoro, ya ce Kotun Daukaka Kara ta yi kuskure da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe, wadda ta ce Abba Gida-Gida bai samu kuri'u mafi rinjaye a zaben 2023 ba.