Kasar Afirka ta Kudu ce ta shigar da karar kan cewa Isra'ila ta karya doka ta hana kisan kare-dangi ta Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1948, wadda aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu da na kisan kare-dangi a Turai. Kotun hukunta manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya ICJ ta umarci Isra'ila da ta dauki dukkan matakan da za ta iya dauka wajen dakile aikata kisan kiyashi a Gaza. A umarnin da kotun ta bayar a ranar Juma'a a ta kuma umarci Isra'ila da ta saukaka ayyukan jinkai a yankin da aka yi wa kawanya. Kotun ICJ ta ce tana da hurumin yanke hukunci kan matakan gaggawa, tana mai cewa ba za ta yi watsi da batun kisan kare-dangi ba kamar yadda Isra'ila ta bukata. Kazalika ta bayyana Falasdinawa a matsayin wata al'umma da ke da kariya a karkashin yarjejeniyar kisan kare-dangi, tana mai jaddada cewa ta amince da hakkin Falasdinawa a Gaza na samun kariya daga ayyukan kisan kare-dangi. A ranar 29 ga watan Disamba ne kasar Afirka ta Kudu ta shigar da kara a gaban kotun ICJ inda ta bukaci a hukunta Isra'ila saboda harin da take kaiwa Gaza ya sabawa yarjejeniyar kisan kare-dangi.. Daga cikin bukatun matakan da Afirka ta Kudu ta nema, akwai bukatar gaggawa na dakatar da Isra'ila daga kai mumunarn hare-hare wanda ta sanadiyar kashe Falasdinawa sama da 26,000, a cewar hukumomin lafiya na Gaza. Haka kuma kasar ta bukaci kotun ICJ ta ba da umarni a hukumance saboda gaggawar lamarin. Bayan kammala sauraren karar a ranakun 11 zuwa 12 ga watan Janairu, kotun ta fara tattaunawa bayan ta yi nazari kan abubuwan da bangarorin suka gabatar da kuma shaidu.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kotun ICJ ta umurci Isra'ila da ta tabbatar sojojinta ba su aikata kisan kare-dangi a Gaza ba
Kasar Afirka ta Kudu ce ta shigar da karar kan cewa Isra'ila ta karya doka ta hana kisan kare-dangi ta Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1948, wadda aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu da na kisan kare-dangi a Turai. Kotun hukunta manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya ICJ ta umarci Isra'ila...

لمحة سريعة
Kasar Afirka ta Kudu ce ta shigar da karar kan cewa Isra'ila ta karya doka ta hana kisan kare-dangi ta Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1948, wadda aka kafa bayan Yakin Duniya na Biyu da na kisan kare-dangi a Turai. Kotun hukunta manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya ICJ ta umarci Isra'ila...
