A ranar Alhamis da Juma'a Kotun Hukunta Manyan Laifuka da ke birnin Hague za ta soma sauraren karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila a gabanta bisa zargin kisan kare-dangi a Gaza abin da ya saba wa Yarjejeniyar 1948 da ta hana irin wannan kisa. A ranar Alhamis da Juma'a Kotun Hukunta Manyan Laifuka da ke birnin Hague za ta soma sauraren karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila a gabanta bisa zargin kisan kare-dangi a Gaza da kuma neman a tilasta mata tsagaita wuta. Isra'ila ta musanta cewa tana yi wa Falasdinawa kisan kare-dangi duk da yake kawo yanzu ta kashe fiye da mutum 23,000, galibinsu mata da kananan yara, sannan ta jikkata kusan mutum 60,000, haka kuma ta raba kashi 85 cikin dari na mutum miliyan 2.3 da ke Gaza da muhallansu. Kazalika ta rusa fiye da kashi 60 na gine-ginen yankin. Shari'ar da za a soma ranar Alhamis, wadda ka iya kwashe shekara da shekaru ana yinta, za ta kuma mayar da hankali kan halascin kasar Isra'ila wadda Yahudawa suka kirkira bayan kisan kiyashi da 'yan Nazi suka yi musu. Kazalika za ta fito da matsayin Afirka ta Kudu: jam'iyyar da African National Congress da ke mulkin kasar ta dade tana kwantanta gallazawar da Isra'ila ke yi wa al'ummar Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan da irin tarihin kasar wadda Turawa tsiraru suka yi wa mulkin mulaka'u da ya hana bakaken-fata sakat har sai a shekarar 1994 da suka samu 'yanci.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Kotun Hukunta Manyan Laifuka za ta soma sauraren karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila kan kisan kare-dangi a Gaza
A ranar Alhamis da Juma'a Kotun Hukunta Manyan Laifuka da ke birnin Hague za ta soma sauraren karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila a gabanta bisa zargin kisan kare-dangi a Gaza abin da ya saba wa Yarjejeniyar 1948 da ta hana irin wannan kisa. A ranar Alhamis da Juma'a Kotun Hukunta Manyan Laif...

A taƙaice
A ranar Alhamis da Juma'a Kotun Hukunta Manyan Laifuka da ke birnin Hague za ta soma sauraren karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila a gabanta bisa zargin kisan kare-dangi a Gaza abin da ya saba wa Yarjejeniyar 1948 da ta hana irin wannan kisa. A ranar Alhamis da Juma'a Kotun Hukunta Manyan Laif...
