Manyan 'yan siyasa sun soma tsokaci kan hukuncin da wata kotu ta yanke wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump da ya shafi shirga ƙarya kan harkokin kasuwancinsa domin ɓoye toshiyar-baki da ya bayar a kan alaƙarsa da wata mai fitowa a finafinan batsa Wata kotu a Amurka ta samu tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da laifi a kan tuhume-tuhume 34 waɗanda ke da nasaba da shirga ƙarya a harkokin kasuwancinsa domin ɓoye toshiyar-baki da ya bayar game da alaƙarsu da fitacciyar mai fitowa a finafinan batsa wato Stormy Daniels a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar a 2016. Jim kaɗan bayan masu taimaka wa alƙali yanke hukunci na kotun ta birnin New York sun sanar da hukuncin, sai aka riƙa samun martani daga 'yan siyasa na jam'iyyu daban-daban da masu fafutuka da kafofin watsa labarai. Donald Trump Bayan yanke hukuncin, Donald Trump ya ce ba shi "da laifi", sannan ya bayyana hukuncin a matsayin "abin kunya". "Wannan hukunci na cike da maguɗi kuma abin kunya ne. Mutane ne za su yanke hukunci na haƙiƙa ranar 5 ga watan Nuwamba. Kuma sun san abin da ya faru, sannan kowa ma ya san abin da ya faru a nan," in ji Trump a yayin da yake barin kotun. Ya ƙara da cewa, "Ba ni da laifi, amma babu komai. Ina fafutuka ne a kan ƙasarmu. Ina fafutuka a kan kundin tsarin mulkimu." Shugaba Joe Biden Shugaba Joe Biden ya yi martani ne ta hanyar yin tsokaci game da zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe a watan Nuwamba, yana mai cewa, "Hanya ɗaya ta hana Donald Trump komawa ofishin shugaban ƙasa wato Oval Office ita ce: akwatunan zaɓe."
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Kotun Amurka ta samu Donald Trump da laifuka kan tuhume-tuhume 34
Manyan 'yan siyasa sun soma tsokaci kan hukuncin da wata kotu ta yanke wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump da ya shafi shirga ƙarya kan harkokin kasuwancinsa domin ɓoye toshiyar-baki da ya bayar a kan alaƙarsa da wata mai fitowa a finafinan batsa Wata kotu a Amurka ta samu tsohon shugaban ƙasa...

A taƙaice
Manyan 'yan siyasa sun soma tsokaci kan hukuncin da wata kotu ta yanke wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump da ya shafi shirga ƙarya kan harkokin kasuwancinsa domin ɓoye toshiyar-baki da ya bayar a kan alaƙarsa da wata mai fitowa a finafinan batsa Wata kotu a Amurka ta samu tsohon shugaban ƙasa...
