Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kotu a Pakistan ta wanke tsohon Firaiminista Imran Khan kan zargin fallasa sirrin gwamnati

Lamarin dai na da alaƙa da huldar diflomasiyya tsakanin Washington da Islamabad, wanda Imran Khan ya ce wani bangare ne na maƙarƙashiyar da Amurka ta ƙulla na hambarar da gwamnatinsa shekaru biyu da suka wuce. Wata kotu a Pakistan ta wanke tsohon Firaminista Imran Khan daga tuhumar da ake masa da...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:14
Kotu a Pakistan ta wanke tsohon Firaiminista Imran Khan kan zargin fallasa sirrin gwamnati
Kwa muhtasari

Lamarin dai na da alaƙa da huldar diflomasiyya tsakanin Washington da Islamabad, wanda Imran Khan ya ce wani bangare ne na maƙarƙashiyar da Amurka ta ƙulla na hambarar da gwamnatinsa shekaru biyu da suka wuce. Wata kotu a Pakistan ta wanke tsohon Firaminista Imran Khan daga tuhumar da ake masa da...

Lamarin dai na da alaƙa da huldar diflomasiyya tsakanin Washington da Islamabad, wanda Imran Khan ya ce wani bangare ne na maƙarƙashiyar da Amurka ta ƙulla na hambarar da gwamnatinsa shekaru biyu da suka wuce. Wata kotu a Pakistan ta wanke tsohon Firaminista Imran Khan daga tuhumar da ake masa da fallasa sirrin gwamnati. A cikin wani dan takaitaccen hukunci, alkalai biyu na Babbar Kotun Islamabad a ranar Litinin din nan karkashin jagorancin Babban Mai Shari'a Aamer Farooq ya kuma wanke Ministan Harkokin Wajen Khan Shah Mehmood Qureshi, wanda ke da hannu a shari'ar. Wata kotu ta yanke wa mutanen biyu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a shari'ar da aka fi sani da "cypher case." Lamarin dai na da alaƙa da huldar diflomasiyya tsakanin Washington da Islamabad, wanda Khan ya ce wani bangare ne na maƙarƙashiyar da Amurka ta kulla na hambarar da gwamnatinsa shekaru biyu da suka wuce. Khan, wanda ya hau kan karagar mulki a shekarar 2018, ya rasa kuri'ar amincewa da majalisar dokokin kasar ne a watan Afrilun 2022, shekara daya da cika wa'adinsa. Duk da wanke shi, Khan zai ci gaba da zama a gidan yari, bayan da kuma aka yanke masa hukunci a wata shari'ar da ta shafi auren matarsa ​​ta uku, Bushra Khan, wanda ya saɓa wa dokokin Musulunci.