Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kocin Masar ya nemi a bai wa Salah kyautar Ballon d'Or ta bana

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Masar, Hossam Hassan ya ce lokaci ya yi da ƙwallo za ta yi wa Mohamed Salah adalci tahanyar ba wa bamisiren kyautar Ballon d'Or ta bana. Yayin da awanni ne suka rage a ayyana wanda ya zama gwarzon ƙwallo ƙafa na duniya a bana, kocin tawagar ƙasar Masar, Hossam Hassan...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:14
Kocin Masar ya nemi a bai wa Salah kyautar Ballon d'Or ta bana
A taƙaice

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Masar, Hossam Hassan ya ce lokaci ya yi da ƙwallo za ta yi wa Mohamed Salah adalci tahanyar ba wa bamisiren kyautar Ballon d'Or ta bana. Yayin da awanni ne suka rage a ayyana wanda ya zama gwarzon ƙwallo ƙafa na duniya a bana, kocin tawagar ƙasar Masar, Hossam Hassan...

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Masar, Hossam Hassan ya ce lokaci ya yi da ƙwallo za ta yi wa Mohamed Salah adalci tahanyar ba wa bamisiren kyautar Ballon d'Or ta bana. Yayin da awanni ne suka rage a ayyana wanda ya zama gwarzon ƙwallo ƙafa na duniya a bana, kocin tawagar ƙasar Masar, Hossam Hassan ya yi kira da a girmama tauraron ƙwallo na ƙasar, Mohamed Salah. Salah na cikin jerin taurarin ‘yan ƙwallon da za a zaɓa don fitar da wanda zai lashe kyautar Ballon d'Or ta shekarar 2025. Da yake ayyana Salah a matsayin ‘gwarzo abin koyi, Hassan ya ce ɗan wasan da ke buga wa Liverpool ta Ingila, abin koyi ne ga masu neman nasara a fannin ƙwallo a duniya. A kakar bara, Mohamed Salah dai ya ciyo wa Liverpool ƙwallaye 34 a duka gasanni kuma ya taka rawar gani wajen taimaka wa ƙungiyarsa lashe kofin Firimiya. Da wuya Salah ya kai labari