Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Kocin Man United ya musanta cewa Man City ta fi su aji

Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya ce 'kwata-kwata ba haka ba ne', cewa Manchester City ta fi su aji, bayan da tawagarsa ta sha kaye a hannun maƙwabtan nasu da ci 3-1. Kocin Manchester City, Erik ten Hag ya dage kan cewa maƙwabtansu kuma manyan abokan hamayyarsu, Manchester City ba su fi su...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:14
Kocin Man United ya musanta cewa Man City ta fi su aji
Кратко

Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya ce 'kwata-kwata ba haka ba ne', cewa Manchester City ta fi su aji, bayan da tawagarsa ta sha kaye a hannun maƙwabtan nasu da ci 3-1. Kocin Manchester City, Erik ten Hag ya dage kan cewa maƙwabtansu kuma manyan abokan hamayyarsu, Manchester City ba su fi su...

Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya ce 'kwata-kwata ba haka ba ne', cewa Manchester City ta fi su aji, bayan da tawagarsa ta sha kaye a hannun maƙwabtan nasu da ci 3-1. Kocin Manchester City, Erik ten Hag ya dage kan cewa maƙwabtansu kuma manyan abokan hamayyarsu, Manchester City ba su fi su aji ba, duk da shan kashin da suka yi a wasansu na Lahadi da ci 3-1. Erik Ten Hag ya yi wannan ikirari ne bayan da aka yi masa tambaya kan ko galabar da aka yi a kansu ta nuna cewa akwai wagegen bambanci na kwarewa tsakanin kungiyoyin biyu da ke birnin Manchester. A kokarinsa na nuna rashin nasarar tawagarsa ba ya nufin Man City ta kere musu a aji, Ten Hag ya yi nuni kan 'yan wasansa da ke jinya, wadanda ba su samu damar buga wasan ba. Ya kuma ayyana galabar da aka yi kansu a matsayin wata 'yar tazara, duk da cewa Man CIty ta nuna matukar rinjaye a kusan kowane bangare na wasan, tun lokacin da Marcus Rashford ya fara ciyo musu kwallo a farkon wasan. A wasan dai, City ta kere su kusan a duka ma'aunin kwarewa, inda United ta rike kwallo da kaso na 27 kacal cikin 100 inda City take da kaso 73. A yawan bugun kan raga United na da 1 CIty na da 8, a kwakkwaran bugu kuma, United na da 3 City na da 27. A yawan taba kwallo ma, United na da 478, yayin da City ke da 981. Sai a fannin ba da kwallo United na da 305 inda City ke da fasin 801. Haka ma a yawan bugun kwana United ta buga 15, inda City ta buga 2 kacal. Da yake ba da amsa kan kokarin 'yan wasansa, Ten Hag ya ce, "Za mu iya nuna bajinta, kuma mun nuna hakan a wasan karshe na gasar FA, amma dai ranar nan ta City ce, kar ku manta da wannan. Su ne kulob din da suka fi kowa a duniya a yanzu." Sakamakon wasan nasu ya bar Man United a mataki na 6, yayin da CIty ke gaba da su da ratar maki 18, a mataki na 2 a teburin na FIrimiya. Dukkaninsu dai wasanni 11 ne suka rage musu kafin kammala gasar.