"Na yi farin ciki da samun amincewar Shugaban kasa kuma niyyata ita ce in samu damar lashe wannan takara," in ji Harris. Dama tuni ta fara ƙere wa sa'a, kuma a yanzu Kamala Harris na ci gaba da yin zarra bayan da Shugaba Joe Biden ya sanar da janywarsa daga takarar shugabancin Amurka tare da nuna amincewarsa ta tsayawa takararta. Biden ya ba da sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata cewa ya janye daga takarar bayan rashin yin abin a zo a gani a wajen muharar da suka yi shi da Trump, inda a ka ga raunin mai shekara 81 ɗin ɓaro-ɓaro na rashin dacewa da neman tazarce. Harris ita ce mace ta farko, Baƙar fata ko kuma 'yar Kudancin Asiya da ta zama mataimakiyar shugaban kasa. Idan ta zama 'yar takarar jam'iyyar Democrat kuma ta doke dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump a watan Nuwamba, za ta kasance mace ta farko da za ta zama shugabar kasa. A ranar Lahadin da ta gabata ne Biden ya ce zaben Harris a matsayin abokiyar takararsa ita ce "mafi kyawun shawarar da na taɓa yanke" kuma ya amince da ita a matsayin wacce za ta gaje shi. "'Yan Jam'iyyar Democrat - lokaci ya yi da za a haɗa ƙarfi a kayar da Trump," ya rubuta a shafinsa na X. "Lokacin yin hakan ya yi." Rayuwar aiki da faɗi-tashi An haifi Harris ranar 20 ga Oktoban 1964, a garin Oakland na jihar California. Iyayenta sun haɗu duka masu fafutukar kare hakkin jama'a. Garinta da kuma na kusa da shi Berkeley sun kasance cibiyoyin da aka fi fafutukar tabbatar da adalci da yaƙi da wariya, don haka Haris ta amfana da fafutukar ta kowane ɓangare. Ta sha yin magana kan yadda tun tana zanin goyo ake halartar zanga-zanga da ita kuma ta girma a cikin manya "waɗanda suke shafe lokuta suna fita fafutuka don ganin an tabbatar da adalci." A lokacin da take aji ɗaya na firamare a motar bas take zuwa makaranta, a matsayinta na wacce ba cikakkiyar 'yar ƙasa ba da ke neman gurbin karatu a ƙarƙashin makarantun gwamnati. Iyayen Harris sun rabu tun tana ƙarama, kuma ita da ƙanwarta Maya, sun taso a hannun mahaifiyarta. Ta halarci Jami'ar Howard, makarantar Baƙaƙen fata mai tarihi a Washington, kuma ta shiga cikin ƙungiyar Alpha Kappa Alpha sorority, wadda ya zama tushen 'yan'uwantaka da goyon bayan siyasa a tsawon shekaru. Bayan kammala karatun, Harris ta koma yankin San Francisco Bay don halartar makarantar sanin makamar shari'a ta kuma ta zaɓi aiki a matsayin mai gabatar da ƙara, matakin da ya ba danginta masu fafutuka mamaki. Ta ce ta yi imanin cewa yin aiki don kawo canji a cikin tsarin yana da muhimmanci tamkar dai yinfafutukar ko babu aikin. A shekarar 2003, ta yi takarar farko ta siyasa, inda ta zama babbar lauyar gundumar San Francisco na tsawon lokaci. Daukaka a matakin ƙasa Harris ta auri lauyan fannin nishaɗi Douglas Emhoff a cikin 2014, kuma ta zama uwa ga 'ya'yansa biyu, Ella da Cole, waɗanda suke kiran ta da "Momala." Harris ta samu damar da ba kasafai ake samu ba, inda ta samu ci gaba a siyasance lokacin da Sanata Barbara Boxer, wacce ta yi aiki sama da shekaru ashirin, ta sanar da cewa ba za ta sake tsayawa takara a shekarar 2016 ba. A cikin ofis, nan da nan sai Harris ta zama wani ɓangare na ƙalubalantar Trump daga Jam'iyyar Democrat, kuma nan da nan aka san ta sosai saboda tambayoyin da ta dinga jefa wa waɗanda aka tsayar takara. A wani lokaci da ba za a manta da ita ba, ta matsa wa lamba Alkalin Kotun Koli na yanzu Brett Kavanaugh lamba a kan ko ya san wata doka da ta bai wa gwamnati damar yin iko da jikin mutum. Bai iya yin hakan ba, kuma jerin tambayoyin sun matuƙar ƙayatar da mata da masu fafutukar kare hakkin bil'adama. Sama da shekaru biyu bayan ta zama Sanata, Harris ta sanar da yakin neman zabenta na takarar shugaban kasa a Democrat a 2020. Amma kamfen ɗin nata ya ci karo da rikice-rikice kuma ta kasa samun karɓuwa, daga ƙarshe ta fice daga cikin 'yan takarar. Bayan watanni takwas, Biden ya zaɓi Harris a matsayin abokiyar takararsa. Yayin da yake gabatar da ita ga al'ummar kasar, Biden ya yi bayani a kan abin da nadin nata ke nufi ga "kananan 'yan mata bakar fata da launin ruwan kasa wadanda galibi ke jin an yi watsi da su da kuma rashin ƙima a cikin al'ummominsu." "A yau, kawai watakila, suna ganin kansu a karon farko a sabuwar hanya, a matsayin na kusa da shugabannin kasa da mataimakan shugaban kasa," in ji shi. Taimakon Harris da yuwuwar samun kalubale Harris ta bayyana shawarar da Biden ya yanke na janyewa daga takaraa a matsayin "aikin rashin son kai da kishin ƙasa," yana mai cewa "ya fifita jama'ar Amurka da kasarmu a kan komai." "Na yi farin ciki da samun amincewar Shugaban kasa kuma niyyata ita ce in samu damar lashe wannan takara," in ji Harris. "A cikin shekarar da ta gabata, na zagaya ko ina cikin kasar, ina tattaunawa da Amurkawa game da zabin da ya dace su yi a wannan gagarumin zaɓe." Fitattun 'yan jam'iyyar Democrat sun bi sawun Biden ta hanyar nuna goyon bayansu ga Harris ba tare da ɓata lokaci ba a ranar Lahadi. Duk da haka, zaɓar tata ba shi ne ƙarshe ba, saboda an kuma ba da shawarar cewa ya kamata jam'iyyar ta gudanar da "zaɓen fitar da gwani" cikin sauri don yin la'akari da sauran 'yan takara kafin babban taronta a Chicago a wata mai zuwa. Wata ƙuri'ar jin ra'ayi ta baya-bayan nan daga Cibiyar Nazarin Harkokin Jama'a ta AP-NORC ta gano cewa kusan mutum shida cikin 10 na 'yan Democrat sun yi imanin Harris za ta yi aiki mai kyau a cikin babban matsayi. Kusan biyu cikin 10 na Democrat ba su yarda da ita ba, kuma wani 2 a cikin 10 sun ce ba su da wani tsayayyen ra'ayi. Binciken ya nuna cewa kusan huɗu cikin 10 manya na Amurka suna da ra'ayin Harris, wadda ake mata laƙabi da "COMM-a-la," yayin da kusan rabin ba sa ra'ayinta.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Ko Kamala Harris na iya zama shugabar ƙasar Amurka mace baƙar fata ta farko?
"Na yi farin ciki da samun amincewar Shugaban kasa kuma niyyata ita ce in samu damar lashe wannan takara," in ji Harris. Dama tuni ta fara ƙere wa sa'a, kuma a yanzu Kamala Harris na ci gaba da yin zarra bayan da Shugaba Joe Biden ya sanar da janywarsa daga takarar shugabancin Amurka tare da nuna...

At a glance
"Na yi farin ciki da samun amincewar Shugaban kasa kuma niyyata ita ce in samu damar lashe wannan takara," in ji Harris. Dama tuni ta fara ƙere wa sa'a, kuma a yanzu Kamala Harris na ci gaba da yin zarra bayan da Shugaba Joe Biden ya sanar da janywarsa daga takarar shugabancin Amurka tare da nuna...
