Wasu manyan laifukan kisan kai da suka jawo hankalin jama’a a Kano cikin ‘yan shekarun nan A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, an rika samun rahotannin kisan-gilla a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, lamarin da ke jawo hankalin jama’a matuƙa. Duk da cewa irin waɗannan laifuka na faruwa a faɗin ƙasar, amma wasu daga cikin waɗanda suka faru a Kano sun fi tayar da hankali saboda yanayinsu na ban tausayi ko kuma abubuwan da suka tattaro ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma. Ɗaya daga cikin abubuwan da suka girgiza jama’a shi ne kisan Fatima Abubakar mai shekara 35 da ‘ya’yanta shida a unguwar Dorayi Charanchi a watan Janairun 2026. Rahotanni sun nuna cewa an kashe su da muggan makamai. Bayan faruwar lamarin, rundunar ‘yansandan jihar ta kama mutane uku da ake zargi, yayin da bincike ke ci gaba. Haka kuma a shekarar 2023, an samu ce-ce-ku-ce kan kisan wani matashi mai suna Nafiu Hafiz, inda ake zargin wata matar aure mai suna Hafsat da aikata laifin. Lamarin ya ja hankalin jama’a sosai bayan bayanai daban-daban da suka rika bayyana a shafukan sada zumunta game da abin da ya faru a gidansu da ke Unguwa Uku a Kano. Wani lamari mai matuƙar tayar da hankali shi ne kisan yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa. Bayan bincike da shari’a, Babbar Kotun Kano ta yanke wa malaminta Abdulmalik Tanko hukuncin kisa bayan samunsa da laifin sace ta da kashe ta. Rahotanni sun nuna cewa ya haɗa kai da wasu wajen sace yarinyar kafin daga bisani ya kashe ta. A shekarar 2022 kuma, kisan budurwa Ummulkulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita, ya jawo muhawara mai zafi a tsakanin jama’a. An zargi wani ɗan ƙasar China mai suna Geng Quangron da bin ta har gidansu a unguwar Janbulo inda ya soka mata wuka har ta rasu. Daga baya ya amsa laifin a gaban kotu. Hakazalika, a shekarar 2020 an samu wani lamari mai ban mamaki lokacin da ake zargin wata uwa ta kashe ‘ya’yanta biyu a unguwar Sagagi. Rundunar ‘yansanda ta tabbatar da mutuwar yaran biyu, Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da Zahra’u Ibrahim mai shekara uku. Rahotanni sun nuna cewa iyayen matar sun bayyana cewa tana fama da tabin hankali tsawon shekaru. Tushen labari: Newstimehub
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Kisan-Gilla Biyar Da Suka Girgiza Jihar Kano
Wasu manyan laifukan kisan kai da suka jawo hankalin jama’a a Kano cikin ‘yan shekarun nan A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, an rika samun rahotannin kisan-gilla a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, lamarin da ke jawo hankalin jama’a matuƙa. Duk da cewa irin waɗannan laifuka na faruwa a faɗi...

Кратко
Wasu manyan laifukan kisan kai da suka jawo hankalin jama’a a Kano cikin ‘yan shekarun nan A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, an rika samun rahotannin kisan-gilla a Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, lamarin da ke jawo hankalin jama’a matuƙa. Duk da cewa irin waɗannan laifuka na faruwa a faɗi...
