Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kiristoci Falasɗinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma

Falasɗinawa mabiya addinin Kirista sun gudanar da bikin Kirsimeti a karon farko tun 7 ga Oktoban 2023, lamarin da ya sa aka dakatar da bikin saboda hare-haren Isra’ila a Gaza da Gaɓar Yamma. Dubban Kiristoci Falasdinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a bainar jama'a a Gaza da aka yi wa ƙawany...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:14
Kiristoci Falasɗinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza da Gaɓar Yamma
De un vistazo

Falasɗinawa mabiya addinin Kirista sun gudanar da bikin Kirsimeti a karon farko tun 7 ga Oktoban 2023, lamarin da ya sa aka dakatar da bikin saboda hare-haren Isra’ila a Gaza da Gaɓar Yamma. Dubban Kiristoci Falasdinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a bainar jama'a a Gaza da aka yi wa ƙawany...

Falasɗinawa mabiya addinin Kirista sun gudanar da bikin Kirsimeti a karon farko tun 7 ga Oktoban 2023, lamarin da ya sa aka dakatar da bikin saboda hare-haren Isra’ila a Gaza da Gaɓar Yamma. Dubban Kiristoci Falasdinawa sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a bainar jama'a a Gaza da aka yi wa ƙawanya da kuma Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye a karon farko tun bayan fara kisan ƙare-dangi a yankin a watan Oktoban 2023. A cikin shekaru biyu da suka gabata, an dakatar da bukukuwan Kirsimeti a Gaza saboda zaluncin Isra'ila. Ko dai an rufe su ko kuma an soke su gaba ɗaya a Gaɓar Yamma da aka mamaye don nuna goyon baya ga Falasɗinawa a yankin da aka yi wa ƙawanya. A Bethlehem, wurin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, dubban mutane sun yi tattaki a kan tituna, tare da bukukuwa cike da murna, suna sanye da kayan Santa Claus suna kiɗa da waƙa. A Gaza, domin bikin Kirsimeti, Falasɗinawa sun je Cocin Iyali Mai Tsarki, wadda ta lalace sakamakon hare-haren Isra'ila kuma ta zama mafaka ga Falasɗinawa da aka raba da gidajensu.