Kenya ta ƙuduri aniyar aika jami'an tsaro 1,000 da za su jagoranci shirin Majalisar Ɗinkin Duniya don tabbatar da tsaro a yankin ƙasashen Caribbean waɗanda rikice-rikice da talauci da kuma rashin kwanciyar hankali na siyasa suka yi wa katutu. Ƙasar Kenya na shirin aika jami'an ‘yan sandanta zuwa Haiti nan da 'yan wasu makwanni domin magance tashe-tashen hankula da suka mamaye ƙasar da ke yankin Caribbean. Za ta ɗauki matakin ne bayan jinkirin da aka samu sakamakon ƙalubalen kotu, a cewar shugaban ƙasar Kenya William Ruto. "Al'ummar Haiti suna jira, da yardar Allah, wataƙila nan da mako mai zuwa ko kuma mako na gaba, za mu aika da jami'an 'yan sandanmu don dawo da zaman lafiya," in ji Ruto a wani jawabin da ya yi ranar Lahadi. Kenya dai ta ƙuduri aniyar jagorantar shirin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) don tabbatar da tsaron al'ummar yankin ƙasashen Caribbean waɗanda rikice-rikice da talauci da kuma rashin rashin kwanciyar hankali na siyasa suka yi wa katutu. Adawa da shirin aika jami'an tsaron Ƙasar da ke yankin Gabashin Afirka ta shirya tsaf domin tura jami'ai 1,000 don aikin tare da wasu jami'an tsaro daga wasu ƙasashe. Wani ƙuduri da Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi a watan Oktoban bara ne ya amince da shirin, sai dai a watan Janairu wata kotu a Kenya ta jinkirta tura jami'an. A cewar kotun, gwamnati ba ta da hurumin aika jami'an 'yan sanda zuwa ƙasashen waje ba tare da wata yarjejeniya ba. A ranar 1 ga watan Maris ne gwamnatin ta samu damar mallakar yarjejeniyar kana a watan ya wuce ne Shugaba Ruto ya shaida wa BBC cewa Kenya na sa ran aika jami'anta zuwa Haiti a cikin makonni da ke tafe. Sai dai wata ƙaramar jam'iyyar adawa a Kenya ta shigar da sabuwar ƙara don hana wannan ƙuduri na gwamanti. A ranar 12 ga watan Yuni ne babbar kotun ƙasar Kenya za ta yi hukunci a kan batun. Kazalika ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama sun zargi 'yan sandan Kenya da yin amfani da ƙarfin-tuwo da kuma salwantar da rayuwa ba bisa ka'ida ba.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kenya za ta aika jami'anta da za su jagoranci shirin tsaro na MDD a Haiti a 'yan makonni'masu zuwa
Kenya ta ƙuduri aniyar aika jami'an tsaro 1,000 da za su jagoranci shirin Majalisar Ɗinkin Duniya don tabbatar da tsaro a yankin ƙasashen Caribbean waɗanda rikice-rikice da talauci da kuma rashin kwanciyar hankali na siyasa suka yi wa katutu. Ƙasar Kenya na shirin aika jami'an ‘yan sandanta zuwa...

At a glance
Kenya ta ƙuduri aniyar aika jami'an tsaro 1,000 da za su jagoranci shirin Majalisar Ɗinkin Duniya don tabbatar da tsaro a yankin ƙasashen Caribbean waɗanda rikice-rikice da talauci da kuma rashin kwanciyar hankali na siyasa suka yi wa katutu. Ƙasar Kenya na shirin aika jami'an ‘yan sandanta zuwa...
