Kuɗin shigar da ake samu a kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya zai iya kai wa dala biliyan 109.4 a bana, ƙari kan dala biliyan 79.4 da aka samu a bara, kamar yadda rahoton Ma'aikatar Kasuwanci ta Turkiyya ya bayyana. Kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya ya ƙaru da kashi 115.5 daga Lira tiriliyan 1.85 (dala biliyan 79.4) a 2023, kamar yadda rahoton Ma'aikatar Kasuwanci ya bayyana. Yawan saye da sayarwar da aka samu ya ƙaru da kashi 22.3 inda a shekara ake samun ƙarin biliyan 5.87, in ji rahoton da mai taken 'Nazari kan Kasuwanci ta Hanyar Intanet a Turkiyya' da aka fitar a ranar Litinin. Ana hasashen kuɗaɗen da za a samu zai kai dala biliyan 109.4 a wannan shekarar kuma adadin saye da sayarwa zai kai biliyan 6.67. A 'yan shekarun nan yawaitar kasuwanci ta hanyar intanet ya daɗu sosai, daga kashi 10.1 a 2019 zuwa kashi 20.3 a 2023. Adadin gudunmawar da kasuwanci ta intanet ke bayarwa ga kuɗaɗen shigar ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 33.3 a shekara bayan shekara inda ya ƙarkare kan kashi 6.8 a 2023. A yayin da kayayyaki da kayan amfani a cikin gida ƙanana ne suka mamaye kasuwancin intanet a Turkiyya da suka samar da dala biliyan $10, sai kayan lantarki na dala biliyan 5.8. inda tufafi, takalma da kayan gyara su suka kama na dala biliyan 5.41.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya ya ƙaru sama da ninki ɗaya a 2023
Kuɗin shigar da ake samu a kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya zai iya kai wa dala biliyan 109.4 a bana, ƙari kan dala biliyan 79.4 da aka samu a bara, kamar yadda rahoton Ma'aikatar Kasuwanci ta Turkiyya ya bayyana. Kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya ya ƙaru da kashi 115.5 daga Lira tiril...

Em resumo
Kuɗin shigar da ake samu a kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya zai iya kai wa dala biliyan 109.4 a bana, ƙari kan dala biliyan 79.4 da aka samu a bara, kamar yadda rahoton Ma'aikatar Kasuwanci ta Turkiyya ya bayyana. Kasuwanci ta hanyar intanet a Turkiyya ya ƙaru da kashi 115.5 daga Lira tiril...
