Zaɓen ya shafi wa’adin 2026–2028 bayan kuri’ar Majalisar Zartarwa Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na Tarayyar Afirka (AU) ya zaɓi sabbin mambobi shida tare da sake zaɓar wasu hudu bayan kuri’ar da Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar ta kada, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana. TRT Hausa Ƙasashen da aka zaɓa sun haɗa da Benin, Gabon, Lesotho, Morocco, Somalia da Afirka ta Kudu, yayin da aka sake zaɓar Cote d'Ivoire, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Sierra Leone da Uganda. TRT Hausa Wa’adin sabbin mambobin zai fara daga ranar 1 ga Afrilun 2026 zuwa 31 ga Maris 2028, kuma kwamitin na da mambobi 15 gaba ɗaya ba tare da kujeru na dindindin ba, domin ana zaɓe ne bisa daidaiton wakilcin yankuna. TRT Hausa An gudanar da zaɓen ne a zaman Majalisar Zartarwa na 48 da aka yi daga ranar 11 zuwa 12 ga Fabrairu, yayin da ake sa ran Majalisar Shugabannin Ƙasashe da Gwamnatoci ta AU za ta amince da sakamakon a zamanta na 39. TRT Hausa Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na AU na taka muhimmiyar rawa wajen hana rikici, warware rikice-rikice, da kuma daidaita martanin Afirka kan barazanar tsaro da ta’addanci a faɗin nahiyar. TRT Hausa
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
AU ta zaɓi sabbin mambobi 10 na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro
Zaɓen ya shafi wa’adin 2026–2028 bayan kuri’ar Majalisar Zartarwa Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro na Tarayyar Afirka (AU) ya zaɓi sabbin mambobi shida tare da sake zaɓar wasu hudu bayan kuri’ar da Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar ta kada, kamar yadda wata sanarwa ta bayyana. TRT Hausa Ƙasashen da ak...

Кратко