Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kamfanin samar da takalman sanyi na Dr Martens ya sanar da dan Nijeriya a matsayin shugabansa

Ije Nwokorie ne sabon shugaban zartarwa na kamfanin samar da takalman sanyi manya na Dr Martens, a yayin da Kenny Wilson ya bayyana daga wannan shekarar zai sauka daga kan shugabancin kamfanin. Kamfanin Dr Martens ya sanar da shugaban sashen tallata kamfanin Ije Nwokorie a matsayin sabon shugaban...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kamfanin samar da takalman sanyi na Dr Martens ya sanar da dan Nijeriya a matsayin shugabansa
A taƙaice

Ije Nwokorie ne sabon shugaban zartarwa na kamfanin samar da takalman sanyi manya na Dr Martens, a yayin da Kenny Wilson ya bayyana daga wannan shekarar zai sauka daga kan shugabancin kamfanin. Kamfanin Dr Martens ya sanar da shugaban sashen tallata kamfanin Ije Nwokorie a matsayin sabon shugaban...

Ije Nwokorie ne sabon shugaban zartarwa na kamfanin samar da takalman sanyi manya na Dr Martens, a yayin da Kenny Wilson ya bayyana daga wannan shekarar zai sauka daga kan shugabancin kamfanin. Kamfanin Dr Martens ya sanar da shugaban sashen tallata kamfanin Ije Nwokorie a matsayin sabon shugaban zartarwarsu (CEO), bayan da Kenny Wilson ya yanke shawarar hakura da shugabancin kamfanin samar dantakalman na Birtaniya a ranar Talata. Nwokorie asalin dan Nijeriya ne. Kamfanin bai bayyana tsayayyiyar ranar miƙa masa jagorancin kamfanin ba. Dr Martens ya sanar da saukar hannun jarinsa da kashi 30 a ranar Talata wanda faduwa ce msfi girma tun bayan da kamfanin na Birtaniya da ke samar da takalma sau ciki ya yi gargadi kan tunkarar shekara mai wahala a kasuwannin Amurka, wanda hakan babban kalubale ne ga sabon shugaban. Kamfanin na fama da karancin masu sayen takalmansa a Amurka musamman masu sayen sari. Sakamako mara kyau Hannun jarin kamfanin ya fuskanci tarnaki a ‘yan shekarun nan, kuma hakan ya janyo abokin huldarsa na Marathon yin gargadi da kira da a samar da sabbin dabarun kasuwanci a farkon wannan watan. A kasuwancin ranar Talata kamfanin ya fuskanci tangardar raguwar sayayya da kaso 65.5. Dr Martens y ace sakamakonsa na wannan shekarar ya kare a ranar 31 ga Maris 2024, kuma suna fuskantar sabuwar shekara mai tsauri. A wata sanarwa ta daban da kamfanin ya fitar y ace, sakamakonsu na kudade na 2024 zai yi daidai da tsammanin da ake yi musu.