الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kamfanin Emirates ya yi sulhu da gwamnatin Nijeriya, zai ci gaba da tashi daga Legas

A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, Emirate ya ce zai ci gaba da zirga-zirga tsakanin birnen Legas da Dubai daga watan Oktoban bana Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Emirates ya sanar da cewa zai ci gaba da tashi daga Nijeriya daga ranar 1 ga Okto...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kamfanin Emirates ya yi sulhu da gwamnatin Nijeriya, zai ci gaba da tashi daga Legas
لمحة سريعة

A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, Emirate ya ce zai ci gaba da zirga-zirga tsakanin birnen Legas da Dubai daga watan Oktoban bana Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Emirates ya sanar da cewa zai ci gaba da tashi daga Nijeriya daga ranar 1 ga Okto...

A wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, Emirate ya ce zai ci gaba da zirga-zirga tsakanin birnen Legas da Dubai daga watan Oktoban bana Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Emirates ya sanar da cewa zai ci gaba da tashi daga Nijeriya daga ranar 1 ga Oktoban wannan shekara. Emirate ya sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, inda ya ce daga nan zai dinga tashi kowace rana tsakanin tsakanin birnin Legas na Nijeriya da Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Mataimakin kamfanin na Emirates Adnan Kazim ya ce "Muna farin cikin dawo da tashin jiragenmu zuwa Nijariya." "Bisa al'ada hanyar Lagos-Dubai ta yi fice a wajen abokan hulɗarmu a Nijeriya," a cewar Adnan. We’re back Nigeria! We’ll be resuming services to Lagos from 1 October 2024, and we can’t wait to offer unrivalled connectivity to Dubai and beyond to over 140 cities. https://t.co/EXGK0g1CnA pic.twitter.com/0AWJpWbBah — Emirates (@emirates) May 16, 2024 Ya kara da cewa "Muna godewa gwamnatin Nijeriya saboda haɗin kai da taimako wajen sake farfaɗo da wannan hanya, sannan muna fatan yin maraba da fasinjojinmu." A watan Agustan 2022 ne, kamfanin na Emirates ya dakatar da safara daga Nijeriya, saboda saɓani da gwamnatin ƙasar wajen fitar da kuɗaɗen kamfanin na cinikin da yake yi daga Nijeriya. Gwamnnatin Nijeriya ta yi marhabin da matakin na Emirates, inda ta ce dama ta daɗe tana jiran wannan rana. "Kamfanin Emirates yi babbar sanarwar a hukumance wacce muke jira, Emirates zai ci dawo Nijeriya a wajen Oktoba," a cewar Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya Festus Keyamo a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Now, the big announcement we have all been waiting for has been officially made by Emirates Airlines:???????? Emirates returns to Nigeria from 1 October https://t.co/VkMoALjNUF — Festus Keyamo, SAN, CON, FCIArb (UK) (@fkeyamo) May 16, 2024