Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. Hukumomi a Isra'ila sun ce za a saki fursunonin yaki 14 'yan Isra'ila da ake rike da su a Gaza da kuma Falasdinawa 42 da ke Isra'ila bayan harin da Hamas ta kaddamar a ranar 7 ga watan Oktoba. Za a saki fursunonin ne a rana ta biyu ta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila. Hukumomin Fursuna sun tabbatar da cewa Falasdinawa 42 - duka maza da mata - za a sake su karkashin yarjejeniyar da aka yi wadda ta amince da yin musanyar Falasdinawa uku da dan Isra'ila daya, kuma wata majiyar gwamnatin Isra'ila ta ce za a mika mutanen 14 da aka yi garkuwa da su.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
KAI-TSAYE: Za a saki 'yan Isra'ila 14 da Falasdinawa 42 a rana ta biyu ta yarjejeniyar musayar fursunoni
Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. Hukumomi a Isra'ila sun ce za a saki fursunonin yaki 14 'yan Isra'ila da ake...