Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda a yau ya shiga kwana na 306, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,653 — yawancinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 91,535, yayin da mutum sama da 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzai Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024 1004 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a yaƙin Isra'ila a Gaza sun kai 39,677 Sojojin Isra'ila sun sake kashe Falasɗinawa 24 a hare-haren da suka kai a faɗin Gaza, lamarin da ya sa yawan mutanen da suka mutu tun daga 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu ya kai 39,677, a cewar Ma'aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya. Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ƙara da cewa zuwa yanzu kuma mutum 91,645 ne suka jikkata. "Dakarun Isra'ila sun kashe mutum 24 tare da jikkata wasu 110 a "kisan kiyashi biyu' da aka yi wa iyalai da dama a cikin awa 24," in ji ma'aikatar. Ta ƙara da cewa "har yanzu akwai mutane da dama da ke binne a ƙarƙashin ɓaraguzai saboda masu aikin ceto sun gaza ciro su." 0652 GMT — Rundunar sojojin Isra'ila ta bayar da sabon umarni ga Falasɗinawan da ke arewacin Gaza su fice daga yankin wanda aka kwashe watanni 10 ana yi wa luguden wuta. Rundunar sojin ta ce za ta mayar da martani ga harin rokokin da Hamas ta harba mata daga yankin Beit Hanoon inda ta umarci mazauna yankin su fice zuwa Birnin Gaza, wani babban yanki da aka riga aka rusa. Beit Hanoon, wanda ke kan iyaka, na cikin wurare na farko da dakarun Isra'ila suka riƙa yi wa luguden wuta babu ƙaƙƙautawa tun da suka ƙaddamar da hare-hare bayan kutsen da ƙungiyar Hamas ta yi a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba. Dakarun Isra'ila suna yawan komawa yankunan da suka lalata ta hanyar yi musu luguden wuta. Isra'ila ta raba galibin al'ummomin Gaza miliyan 2.3 da gidajensu tun lokacin da ta soma kai hare-hare a yankin. Dubbansu suna samun mafaka a tantuna da ke cike da jama'a. 2038 GMT — Hezbollah ta yi murna da naɗin Sinwar a matsayin sabon shugaban siyasa na Hamas Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta taya murna ga Yahya Sinwar bayan naɗinsa a matsayin sabon shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, tana mai cewa matakin ya nuna cewa burin Isra'ila na kashe Ismail Haniyeh bai cika ba. Sinwar zai maye gurbin Ismail Haniyeh, shugaban ɓangaren siyasa na Hamas kuma jagora a tattaunawar neman tsagaita a Gaza, wanda Isra'ila ta yi wa kisan gilla a gidansa da ke Tehran ranar 31 ga watan Yuli jim kaɗan bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Iran. Iran ta sha alwashin mayar da martani kan kisan Haniyeh da gwamnatin Netanyahu ta yi. Zaɓen da aka yi masa a matsayin shugaban Hamas "ya aike da babban saƙo ga masu mamaya (Isra'ila) cewa Hamas za ta ci gaba da gwagwarmaya", a cewar wai sabban jami'in Hamas a hira da kamfanin labarai na AFP. Sinwar zai maye gurbin Ismail Haniyeh, shugaban ɓangaren siyasa na Hamas kuma jagora a tattaunawar neman tsagaita a Gaza, wanda Isra'ila ta yi wa kisan gilla a gidansa da ke Tehran ranar 31 ga watan Yuli jim kaɗan bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Iran. / Hoto: Reuters
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kai-tsaye: Yawan Falasɗinawan da suka mutu a yaƙin Isra'ila a Gaza sun kai 39,677
Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda a yau ya shiga kwana na 306, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,653 — yawancinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 91,535, yayin da mutum sama da 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzai Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024 1004 GMT — Yaw...

Bu haberde ne var?
Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda a yau ya shiga kwana na 306, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,653 — yawancinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 91,535, yayin da mutum sama da 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzai Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024 1004 GMT — Yaw...
