Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 167 - ya kashe Falasdinawa akalla 31,988 tare da raunata wasu 74,188 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 0856 GMT — Yawan Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe ya kai 31,988 Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta bayar da rahoton cewa mutum 65 ne suka mutu a cikin awa 24 da suka gabata sakamakon hare-haren Isra'ila, yayin da wasu 92 suka jikkata. Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce yawan Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe zuwa yanzu tun bayan fara yaƙin ranar 7 ga watan Oktoban bara, ya kai 31,988, yayin da yawan waɗanda suka jikkata ya kai 74,188. Hare-haren da Isra'ila ke zafafa kaiwa Falasɗinu na ci gaba da yin mummunan tasiri a kan fararen hula a yankin Gaza. 0812 GMT — Blinken ya gana da Yarima mai jiran gado na Saudiyya don tattaunawa a kan Gaza Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya gana da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman da kuma Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Yarima Faisal bin Farhan don tattaunawa a kan yanayin jinƙai da ake ciki a Gaza da kuma ƙoƙarin ƙara yawan agaji ga Falasɗinawa. Blinken ya fara rangadi ne a yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Laraba.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Kai-tsaye: Yawan Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe ya kai 31,988
Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 167 - ya kashe Falasdinawa akalla 31,988 tare da raunata wasu 74,188 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 0856 GMT — Yawan Falasɗinawan da Isra'ila ta k...

Кратко
Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 167 - ya kashe Falasdinawa akalla 31,988 tare da raunata wasu 74,188 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 0856 GMT — Yawan Falasɗinawan da Isra'ila ta k...
