Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Kai-tsaye: Yarjejeniyar tagaita wutar Gaza za ta fara aiki ranar Lahadi 6:30 na safe agogon GMT — Qatar

Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza inda aka shafe kwanaki 470 ana kisan kiyashi a Gaza, inda aka kashe Falasɗinawa 46,876 da kuma jikkata fiye da 110,642. A Lebanon kuwa Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,068 tun daga Oktobar 2023. 0715 GMT — Yarjejeniyar tsagaita wutar ta Gaza...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
Kai-tsaye: Yarjejeniyar tagaita wutar Gaza za ta fara aiki ranar Lahadi 6:30 na safe agogon GMT — Qatar
En bref

Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza inda aka shafe kwanaki 470 ana kisan kiyashi a Gaza, inda aka kashe Falasɗinawa 46,876 da kuma jikkata fiye da 110,642. A Lebanon kuwa Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,068 tun daga Oktobar 2023. 0715 GMT — Yarjejeniyar tsagaita wutar ta Gaza...

Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza inda aka shafe kwanaki 470 ana kisan kiyashi a Gaza, inda aka kashe Falasɗinawa 46,876 da kuma jikkata fiye da 110,642. A Lebanon kuwa Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,068 tun daga Oktobar 2023. 0715 GMT — Yarjejeniyar tsagaita wutar ta Gaza za ta fara aiki ne a ranar Lahadi da karfe 0630 agogon GMT, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari ya ce "Kamar yadda bangarorin da ke cikin yarjejeniyar da masu shiga tsakani suka shirya, tsagaita bude wuta a zirin Gaza za ta fara aiki da karfe 8:30 na safe a ranar Lahadi 19 ga watan Janairu, agogon kasar." "Muna ba da shawara ga mazauna garin da su yi taka-tsantsan, kuma su jira umarni daga majiyoyin hukuma." 2200 GMT — Shugabannin Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan sun ce a shirye suke su mulki Gaza Shugabanin Falasdinu da ke kula da wasu sassan Yammacin Gabar Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, sun ce a shirye suke "su rinƙa kula da lamura" a Gaza, a cewar wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito. Ofishin shugaban kasar Mahmud Abbas ya ce hukumomin gudanarwa da tsaro na hukumar Falasdinu sun kammala shirye-shiryen maido da muhimman ayyuka a Gaza da Hamas ke mulki. Sai dai har yanzu babu wani shiri na wanda zai mulki Gaza bayan yakin kisan kare dangi na Isra'ila.