Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: 'Yan jam'iyyar Democrat sun yi kira ga Biden ya hana Isra'ila mamaye Rafah

Isra'ila ta kwashe kwana 209 tana yaƙi a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,568 — kashi 70 jarirai ne da ƙananan yara da mata — sannan suka jikkata fiye da mutum 77,765 kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2216 GMT — 'Yan jam'iyyar Democrat sun yi kira...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: 'Yan jam'iyyar Democrat sun yi kira ga Biden ya hana Isra'ila mamaye Rafah
De un vistazo

Isra'ila ta kwashe kwana 209 tana yaƙi a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,568 — kashi 70 jarirai ne da ƙananan yara da mata — sannan suka jikkata fiye da mutum 77,765 kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2216 GMT — 'Yan jam'iyyar Democrat sun yi kira...

Isra'ila ta kwashe kwana 209 tana yaƙi a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,568 — kashi 70 jarirai ne da ƙananan yara da mata — sannan suka jikkata fiye da mutum 77,765 kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2216 GMT — 'Yan jam'iyyar Democrat sun yi kira ga Biden ya hana Isra'ila mamaye Rafah Gwamnatin Shugaba Joe Biden tana shan sabuwar suka daga 'yan jam'iyyar Democrat domin ya hana Isra'ila ƙaddamar da cikakkiyar mamaya a Rafah, birnin da kimanin rabin mutanen Gaza miliyan 2.4 suke samun mafaka. 'Yan majalisar wakilai hamshin da bakwai daga cikin 212 na jam'iyyar Democrat sun rattaba hannu kan wata wasiƙa inda suka yi kira ga gwamnatin Biden ta tsawatar da gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu mai kunnen-ƙashi daga mamayar birnin Rafah da ke kan iyakar Masar. "Muna kira a gare ka da ka ɗauki mataki na doka nan-take don hana duk wani taimako ga gwamnatin Isra'ila, ciki har da tallafin da majalisa ta amince da shi, da zummar hana ƙaddamar da mamaya a Rafah," a cewar wasiƙar da suka rubuta ranar Laraba. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ranar Laraba ya ce har zuwa lokacin bai ga wani shirin Isra'ila na ƙaddamar da mamaya a Rafah ba, yana mai jaddada cewa mahukunta a Washington ba za su "goyi bayan" hakan ba. 0009 GMT — Ɗaliban Jami'ar Fordham ta New York sun kafa sansanin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza Wasu ɗalibai na Jami'ar Fordham da ke Birnin New York sun kafa sansani inda suke nuna goyon baya ga al'ummar Gaza, a wani mataki na bin sawun takwarorinsu a faɗin Amurka da ke kira a kawo ƙarshen hare-haren da Isra'ila take kai wa Falasɗinawa. Ɗalibai da dama sun mamaye Cibiyar Leon Lowenstein, wani gini da ke reshen jami'ar na Lincoln Center, inda suka kafa sansani biyar a wani mataki na nuna goyon baya ga Falasɗinawa. Mahukuntan jami'ar sun aika wa ɗaliban wasiƙa ta hannun shugabar Lincoln Center Jenifer Campbell inda suka umarce su da su fice daga Jami'ar Fordham nan-take. Kazalika jami'ar ta ce za ta dakatar da ɗalibai daga shiga ɗakunansu da ajujuwa da rubuta jarrabawa da ma duk wasu al'amura na jami'ar.