Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: 'Yan Houti sun yi iƙirarin 'kai hari' kan jirgin ruwan Isra'ila a Tekun Arabiya

Isra'ila ta kwashe kwana 264 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,658 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,237, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2123 GMT — Mayaƙan Houti sun ce sun yi amfani da...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: 'Yan Houti sun yi iƙirarin 'kai hari' kan jirgin ruwan Isra'ila a Tekun Arabiya
At a glance

Isra'ila ta kwashe kwana 264 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,658 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,237, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2123 GMT — Mayaƙan Houti sun ce sun yi amfani da...

Isra'ila ta kwashe kwana 264 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,658 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,237, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2123 GMT — Mayaƙan Houti sun ce sun yi amfani da wani sabon makami mai linzami wajen kai hari kan jirgin ruwan MSC Sarah V a Tekun Arabiya, inda suka ɗauki nauyin kai harin da aka bayar da rahotonsa. Yahya Sarea, mai magana da yawun ƙungiyar, ya yi iƙirarin cewa harin "ya afka kuma ba kuskure" kan jirgin ruwan, yana bayyana jirgin da cewa "na Isra'ila" ne. Cibiyar The United Kingdom Maritime Trade Operations ta ce an ba da rahoton cewa ma'aikatan jirgin suna cikin ƙoshin lafiya, sannan jirgin ya nufi tashar da zai tsaya ta gaba. 2225 GMT — Sojojin Amurka sun gayyaci 'yan jarida zuwa shirin kai agaji Gaza ta ruwa Bayan jeka ka dawo da dama, shirin nan na kai agaji Gaza na $230 miliyan ya dawo ka'in da na'in. Rundunar sojan Amurka ta gayyaci 'yan jarida zuwa wata ziyara, wacce ta zama karon farko da 'kafofin watsa labari na duniya suka shaida yadda ake aikin agajin. Yayin da 'yan jarida ke duba abin da ke faruwa, su kuma sojojin Amurka riƙe da bindigogi ƙirar mashinga suna jagorantar aikin. Jiragen Amurka maƙale da kayan agaji sun tsaye a wajen. Isra'ila ta hana 'yan jaridar ƙasashen waje kawo rahotannin yaƙin da ake yi a Gaza, mafi yawan labaran 'yan jarida Falasɗinawa na cikin gida ne suke bayar da su. Isra'ila ta kashe fiye da 'yan jarida 150, ta kuma jikkata wasu gommai tun daga watan Oktaban bara.