Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 338, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,000 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Lahadi, 8 ga September 2024 0140 GMT — Ƙungiyar Houthi ta Yamen ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin Amurka mara matuƙi da ke "kai hare-hare" a tsakiyar Yamen. Mai magana da yawun dakarun Houthi Yahya Sarea ya ce tsaron Yemen na sama "ya samu nasarar" kakkaɓo jirgin Amurka mara matuƙi MQ-9 a sararin samaniyar Marib. Sarea ya tabbatar da cewa dakarun Houthi sun ci gaba da sauke nauyinsu "na goyon bayan wahalar da Falasaɗinawa suke sha da kuma tsare Yamen." A wani ɓangare na jaddada goyon baya ga Gaza, wanda ke fuskantar munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa tun daga 7 ga Oktoba, 'yan Houthi sun ringa kai hare-hare da makamai masu linzami da da jirage masara matuƙa kan jiragen ruwan Isra'ila ko waɗanda ke da alaƙa da Isra'ila da ke bi ta Bahrul Aswad, da Bahar Maliya da Tekun India, Tun daga farkon 2024, wani ƙawance da Amurka ke jagoranta ya ringa kai hare-hare ta sama suna da'awar kai wa wuraren da 'yan Huti suke hare-hare a Yemen a matsayin martani ga hare-haren teku, waɗanda a wasu lokutan 'yan Houthi suke mayar da martani.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-Tsaye: 'Yan Houthi sun ce sun harbo jirgin Amurka mara matuƙi MQ-9 a Yemen a lokacin da ake ci gaba da yaƙin Gaza
Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 338, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,000 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Lahadi, 8 ga September 2024 0140 GMT — Ƙungiyar Houthi ta...

لمحة سريعة
Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 338, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,000 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Lahadi, 8 ga September 2024 0140 GMT — Ƙungiyar Houthi ta...
