Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: 'Yahudawa 'yan kama wuri zauna da sojojin Isra'ila sun kai hari Yammacin Kogin Jordan

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 345, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,182 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,280 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0420 GMT — Yahudawa 'yan kama wuri zauna tare da haɗin gwiwa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: 'Yahudawa 'yan kama wuri zauna da sojojin Isra'ila sun kai hari Yammacin Kogin Jordan
Kwa muhtasari

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 345, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,182 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,280 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0420 GMT — Yahudawa 'yan kama wuri zauna tare da haɗin gwiwa...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 345, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,182 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,280 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0420 GMT — Yahudawa 'yan kama wuri zauna tare da haɗin gwiwar sojojin Isra'ila sun afka ƙauyuka da birane da dama a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a ranar Asabar da dare, wanda hakan ya sa suka yi fito-na-fito da Falasɗinawa. Gidan talabijin na Falasɗinu ya bayar da rahoton cewa an jikkata mutum guda a lokacin samamen da 'yan kama wuri zauna suka kai waɗanda sojojin na Isra'ila ke ba su kariya a ƙauyen Umm Safa da ke arewacin Ramallah. Sai dai rahoton bai yi bayani kan irin raunin da aka ji wa mutumin ba. Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu Wafa ya yi nuni da cewa, wasu da dama daga cikin 'yan kama wuri zaunansun afka Umm Safa, inda suke harba harsasai a kan gidajen mutane. 0504 GMT — Aƙalla Falasɗinawa hudu aka kashe a harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza. Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu Wafa ya ce jiragen yaki sun yi ruwan bama-bamai a yankin da ke kusa da mahadar Abu Sarrar da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza. Falasdinawa uku ne suka mutu a harin, yayin da motocin sojin Isra'ila kuma suka yi luguden wuta mai tsanani kan sansanin. Sojojin sun kuma kai hari kan wani gida na iyalan Suweidan a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke arewacin Gaza.