Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

KAI-TSAYE: WHO ta ce ta kasa tuntubar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa

Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0940 GMT — Sojojin Isra'ila sun kara kashe wani matashi a Gabar Yamma da Kogi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
KAI-TSAYE: WHO ta ce ta kasa tuntubar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa
Bu haberde ne var?

Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0940 GMT — Sojojin Isra'ila sun kara kashe wani matashi a Gabar Yamma da Kogi...

Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0940 GMT — Sojojin Isra'ila sun kara kashe wani matashi a Gabar Yamma da Kogin Jordan Sojojin Isra’ila sun kara kashe wani Bafalasdine a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Lahadi, lamarin da ya ja adadin Falasdinawan da aka kashe a gabar ya kai 186, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta tabbatar. Israeli occupation forces shot and kill the Palestinian man identified as Muntaser Seif in the town of Burqa, north of the occupied West Bank. #GazaGenocide #Gazagenocide #GazaUnderaAttack #Gaza_under_attack #غزة #غزة_تُباد #غزه_تحت_القصف_ pic.twitter.com/BSPOJcB3Lg — Wafa News Agency - English (@WAFANewsEnglish) November 12, 2023 A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce “Sojojin Isra’ila sun harbe Montaser Muhammad Amin Saif mai shekara 34 a ranar Lahadi a kauyen Burqa da ke arewacin Nablus.” Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ce sojojin sun shiga kauyen na Burqa inda suka yi bincike a gidaje da dama. 0910 GMT — WHO ta ce ta kasa tuntubar asibitin Al-Shifa na Gaza saboda yanke hanyoyin sadarwa Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus a safiyar Lahadi ya tabbatar da cewa babu wata hanya da kungiyarsa ta WHO za ta tuntubi asibitin Al-Shifa da ke Zirin Gaza. “WHO ta rasa hanyoyin sadarwa tsakaninta da cibiyarta da ke Asibitin Al-Shifa da ke Gaza, a daidai lokacin da ake samun rahotanni masu ban tsoro na karin hare-hare,” kamar yadda Tedros ya bayyana a shafin X. Mista Tedros ya bayyana cewa wasu rahotanni sun ce wasu da suka gudu daga asibitin an harbe su inda aka kashe su, wasu kuma an ji musu rauni.