Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Wani makamin roka da aka harba daga Lebanon ya jikkata mutum 19 a Isra'ila

Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 392 - ya kashe kusan mutum 43,259 da jikkata fiye da 101,820, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,865 tun daga Oktoban bara. 0927 GMT — Wani makamin roka da aka harba daga Leban...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Wani makamin roka da aka harba daga Lebanon ya jikkata mutum 19 a Isra'ila
A taƙaice

Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 392 - ya kashe kusan mutum 43,259 da jikkata fiye da 101,820, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,865 tun daga Oktoban bara. 0927 GMT — Wani makamin roka da aka harba daga Leban...

Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 392 - ya kashe kusan mutum 43,259 da jikkata fiye da 101,820, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,865 tun daga Oktoban bara. 0927 GMT — Wani makamin roka da aka harba daga Lebanon ya jikkata mutum 19 a Isra’ila bayan makamin ya faɗa kan wani gini a garin Tira a ranar Asabar. Sojojin Isra’ila sun bayar da rahoton ƙarar jiniya a yankunan Sharon da Dan a daidai lokacin da aka harba makaman roka uku daga Lebanon inda suka shiga sararin samaniyar Isra’ila. Duk da cewa an yi ƙoƙarin daƙile makaman, akwai ɗaya daga cikin makaman da ya wuce inda ya faɗa a cikin Isra’ilar. Rundunar sojin ta kuma ce an harba rokoki 10 daga kasar Lebanon zuwa yankunan Haifa Bay da Galili a arewacin Isra'ila. An daƙile wasu, yayin da wasu suka fadi a wuraren da babu gidaje. 0703 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 8 a arewaci da tsakiyar Gaza Akalla Falasdinawa 8 ne suka rasu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a arewaci da tsakiyar Gaza. Majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Falasdinawa uku ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata lokacin da sojojin Isra'ila suka kai hari a unguwar Saftawi da ke arewacin birnin Gaza. A gefe guda kuma, kanfanin dilancin labaren Falasdinawa WAFA ya bayar da rahoton cewa, harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai wa wani ginin mazaunin sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza ya kashe mutum biyar tare da jikkata wasu da dama.