Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 291 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,006 — yawancinsu mata da yara –– tare da jikkata mutum sama da 89,818, yayin da mutum fiye da 10,000 ke binne a ɓaraguzai. 0431 GMT –– Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi ya yaba game da matakin da ƙungiyoyin Falasɗinawa 14 suka amince da shi na kafa "gwamnatin riƙon-ƙwarya ta haɗin-kan ƙasa" da za ta jagoranci Gaza bayana yaƙi. Ɓangagorin da suka haɗa da ƙungiyar Hamas da Fatah sun gana a Beijing a wannan makon a wani sabon yunƙuri na yin sulhu a tsakaninsu. A yayin da ake kammala taron, Ministanr Harkokin Wajen China ya ce ɓangarorin sun amince su yi "sulhu". "Babbar nasarar da aka samu ita ce amincewar da aka yi a kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ta haɗin-kan ƙasa domin gudanar da mulkin Gaza bayan kammala yaƙi," in ji Wang jim kaɗan bayan ɓangarorin sun sanya hannu a kan "Yarjejeniyar Beijing" a babban birnin China. "Sulhu abu ne da ya kamata ɓangarorin Falasɗinawa su yi a cikin gida, amma kuma a lokaci ɗaya, ba za a iya cim masa ba, ba tare da goyon bayan ƙasashen duniya," a cewar Wang. 2100 GMT — Masu goyon bayan Falasɗinawa a Amurka sun yi zanga-zanga kan zuwan Netanyahu ƙasar Masu goyon bayan Falasɗinawa a Amurka sun taru a wajen otal ɗin Watergate da ke Washington DC, inda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sauka gabanin ya yi jawabi ga zauren majalisar dokokin ƙasar ranar Laraba. Masu zanga-zangar suna riƙe da kwalaye da aka rubuta: "A kama Netanyahu" da kuma "Mai laifin yaƙi yana cikin wannan otal ɗin," sua nufin Firaminista Netanyahu wanda ke da alhakin kisan dubban Falasɗinaa fararen-hula a Gaza. Kazalika ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zangar ranar Laraba a yayin da Netanyahu zai gabatar da jawabi ga 'yan majalisar dokokin Amurka a yayin da ƙasarsa ke ci gaba da luguden wuta a Gaza. Kazalika ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zangar ranar Laraba a yayin da Netanyahu zai gabatar da jawabi ga 'yan majalisar dokokin Amurka a yayin da ƙasarsa ke ci gaba da luguden wuta a Gaza. 2222 GMT — Biden ya sha alwashin 'ci gaba da aiki domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza' Shugaban Amurka Joe Biden ya sha alwashin ci gaba da aiki domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin Gaza har zuwa ƙarshen wa'adinsa na mulki bayan ya fasa sake tsayawa takara. "Zan ci gaba da aiki kafaɗa-dakafaɗa da Isra'ila da Falasɗinawa domin ƙoƙarin ganin yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, da kuma tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, tare da tabbatar da ganin waɗanda aka yi garkuwa da su sun koma gida," in ji Biden a wani jawabi da ya yi a hedkwatar yaƙin neman zaɓensa, wadda ya mayar ta goyon bayan takarar shugabancin ƙasar mataimakiyarsa Kamala Harris.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Wani ɓangare na Falasɗinawa ya amince ya kafa gwamnatin haɗin-kai a Gaza
Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 291 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,006 — yawancinsu mata da yara –– tare da jikkata mutum sama da 89,818, yayin da mutum fiye da 10,000 ke binne a ɓaraguzai. 0431 GMT –– Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi ya yaba game da mat...

Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 291 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,006 — yawancinsu mata da yara –– tare da jikkata mutum sama da 89,818, yayin da mutum fiye da 10,000 ke binne a ɓaraguzai. 0431 GMT –– Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi ya yaba game da mat...
